Duk da matsin lamba, ba za mu yi karyar bullar cutar korona ba a jihar Kogi - Dr Haruna

Duk da matsin lamba, ba za mu yi karyar bullar cutar korona ba a jihar Kogi - Dr Haruna

Kwamishinan lafiya na jihar Kogi, Dr Saka Haruna, ya bayyana cewa, duk da huro wutar da ake yi wa gwamnatin jihar gami da matsin lamba, ba za ta yi karyar bullar cutar korona ba a jihar.

Kwamishinan ya ce duk wata tilastawa da wani matsin lamba, ba zai sa gwamnatin Kogi ta ayyana bullar cutar korona ba alhalin babu cutar a jihar.

Furuncin kwamishinan ya zo ne cikin wata sanarwar da ya gabatar wa manema labarai a ranar Alhamis kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Dr Haruna ya yi martani dangane da jita-jitar da ke yaduwa a jihar ta cewa ana zargin cutar korona ce ta kassara wasu mutane hudu da suka riga mu gidan gaskiya a cibiyar lafiya ta tarayya da ke Lakwaja, a cikin makon da ya gabata.

A cewarsa, dukkanin masu wannan matsin lamba a jihar, 'yan siyasa ne da ke adawa da gwamnatin jihar mai ci a yanzu.

Ya kara da cewa, a matsayinsa na kwamishinan lafiya a jihar, kuma daya daga cikin mambobi masu kula da cibiyar lafiyar ta Lakwaja, baya ga kasancewarsa jagoran masu lura da annobar korona a jihar, ba ya da masaniyar an samu koda mutum guda da ya kamu da cutar.

A makon nan ne dai gwamnatin jihar Kogi ta ce ta gano tuggun da ake kullawa na neman ta dole sai an shigo da kwayoyin cutar korona cikin jihar ta kowace irin haramtacciyar hanya.

Gwamnan jihar Kogi; Yahaya Bello

Gwamnan jihar Kogi; Yahaya Bello
Source: Facebook

Gwamnatin jihar ta ce wannan yana daya daga cikin makarkashiyar da ake kulla wa na neman sai an tursasawa kowace jiha a fadin Najeriya samun bullar cutar.

Ta yi zargin cewa "a baya-bayan nan akwai miyagun da ke ci gaba da matsin lamba ta lallai sai an lalubo masu cutar tare da kaddamar da bullar ta a jihar."

A rahoton da jaridar Premium Times ta ruwaito, gwamnatin Kogi ta yi zargin yadda wasu masu wannan mummunar bukata ke huro wutar ayyana samun bullar cutar a jihar.

KARANTA KUMA: Tallafin rage nauyin bashi: Buhari ya gana da Firai Ministan Pakistan

Sai dai fa gwamnatin ba ta fayyace ainihin masu neman kulla tuggun da zai shuka wannan mummunar badakala ba.

Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata, kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar, Kingsley Fanwo, ya yi zargin cewa, akwai yunkurin sai lallai an shigo da wannan annoba jihar Kogi.

Jihar da ke yankin Arewa ta Tsakiya, tana kewaye ne da jihohin da tuni suka samu bullar annobar ta korona.

An samu bullar cutar korona cikin dukkanin jihohin Arewa ta Tsakiya in banda jihar Kogi.

A yanzu haka jihar tana ci gaba da fafatawa da gwamnatin tarayya dangane da yadda har kawo yanzu ta ke ikirarin bata samu bullar cutar ba.

Gwamnatin jihar cikin sanarwar da ta fitar ta bayyana cewa, babu yadda za a yi ta fidda bayanan karya ko kuma ta yi kagen samun bullar cutar domin biyan bukatar wasu jami'an lafiya da bata ambaci sunansu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel