COVID-19: Daya daga cikin hadiman Trump ya kamu da korona

COVID-19: Daya daga cikin hadiman Trump ya kamu da korona

Wani sojan Amurka da ke yi wa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump hidima ya kamu da coronavirus.

Amma mai magana da yawun gwamnatin kasar, Hogan Gidley a cikin wata sanarwa ya ce, "shugaban kasar da mataimakinsa ba su kamu da cutar ba kuma suna cikin koshin lafiya."

Mataimakin shugaban kasa Mike Pence yana tare da wata tawaga da ke raba wa cibiyar sauya halayen mutane a kasar magunguna da kayan asibiti a lokacin da labarin ya fito.

Trump yana birnin Washington kuma akwai wasu tarurruka da zai hallarta a ranan kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

COVID-19: Daya daga cikin hadiman Trump ya kamu da korona
COVID-19: Daya daga cikin hadiman Trump ya kamu da korona. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Ke duniya: An damke mutumin da ya birne mahaifiyarsa da ranta

Kafar watsa labarai ta CNN ta ce wanda ya kamu da cutar jamii ne a Rundunar Sojojin Ruwan Amurka da ke kula da tufafi da wasu kayayyakin Trump.

Rahotanni sun ce ana yi wa manyan wadanda ke aiki a fadar shugaban kasar ta White House gwajin korona lokaci zuwa lokaci.

Manema labarai da ke cudanya da jamian na White House su ma akan yi musu gwaji na duba yanayin zafin jikinsu kafin a bari su shiga dakin da manema labarai ke gana wa da jami'an gwamnati.

A wani rahoton, kun ji cewa, an birne wata tsohuwar ma'aikaciyar gwamnati wacce ta yi murabus mai suna Wanng da ranta na kwanaki uku.

Kamar yadda jaridar metro.co.uk ta wallafa, danta mai shekaru 57 ne ya birne ta. Hukumomi a Jingbian da ke yankin Shaanxi a arewa maso yamma na kasar China sun garzaya inda aka birne matar bayan sun samu rahoto daga sirikar tsohuwar.

An ga yadda jami'an suka fito da tsohuwar mai shekaru 79 daga cikin tabo amma kuma tana numfashi. A halin yanzu, dan na hannun hukuma inda ake tuhumarsa da yunkurin kisan kai.

Masu bincike sun bayyana cewa ya saka mahaifiyarsa a keken guragu inda ya fitar da ita daga gida wurin karfe 8 na daren Asabar.

Ya dawo gida babu ita a sa'o'in farko na safiyar Lahadi amma ba tare da tsohuwar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel