COVID-19: Ci gaban mace-mace a Yobe ya jawo cece-kuce

COVID-19: Ci gaban mace-mace a Yobe ya jawo cece-kuce

A kalla mutum 155 aka gano sun rasu a jihar Yobe a kwanaki shida da suka gabata bayan bayyanar alamar annobar Coronavirus.

Mace-macen da ke faruwa a garin Gashua da Potiskum sun janyo tsoro a zukatan jama'ar jihar don yanayin hakan ne ya fara a jihar Kano.

Wani mazaunin jihar wanda ya yi magana da jaridar New Telegraph, ya ce a makon da ya gabata an samu rashin rayuka 98 a Potiskum yayin da 57 suka rasu a Gashua.

"Makabartu a halin yanzu sun fi ko ina zama wurin cunkoso. Dattijai masu shekaru da yawa na ta rasuwa. Amma kuma kwamitin yaki da COVID-19 na jihar na baccinsu a Damaturu tamkar babu abinda ke faruwa," majiyar tace.

Sun zargi Gwamna Mai Mala Buni da barin nauyin da ke kansa tare da tarewa a Abuja.

A martanin gaggawa da gwamnatin jihar Yobe tayi, ta musanta rahoton mace-macen da kuma tarewar gwamnan a Abuja.

Buni, wanda ya musanta rahoton ya yi kira ga jama'ar jihar da su yi watsi da labaran.

COVID-19: Ci gaban mace-mace a Yobe ya jawo cece-kuce
COVID-19: Ci gaban mace-mace a Yobe ya jawo cece-kuce. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: Yadda aka tilasta wa limamai share gidan hakimi a Kano

Kamar yadda wata takarda da ta fita a ranar Alhamis, Mamman Mohammed, mataimaki na musamman ga gwamna Mai Mala Buni a fannin yada labarai, ya ce an fara samun bullar cutar ne a karon farko a makon da ya gabata a jihar.

Mohammed ya sake musanta ikirarin da ake yi na cewa Buni ya bar jihar inda ya koma Abuja. Ya ce gwamnan ya tafi babban birnin tarayyar ne don ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

"Domin karin bayani, jihar Yobe ce ta fara aika wa da samfur na wanda take zargin yana dauke da cutar amma aka yi sa'a baya dauke da ita," hadimin yace.

"Duk da ba a samu cutar a jihar ba, gwamnatin ta kafa kwamitin, ta samar da cibiyar killacewa tare da duk kayayyakin aikin da ya dace.

"An fara samun bullar cutar a jihar Yobe a ranar 30 ga watan Afirilun 2020 amma kuma babu wanda ya taba rasuwa sakamakon cutar.

"Abu na biyu, Gwamna Buni bai fita jihar ba na tsawon makonni shida har sai da shugaba Buhari ya gayyacesa Abuja don tattaunawa a kan lamarin tsaro na jihar. Kwanaki uku kacal ya yi kuma ya dawo Yobe.

"A don haka, yana nan cikin jihar yana mulkinsa ba kamar yadda ake ta rade-radi ba.

"Gwamnatin jihar na kira ga manema labarai da su nemi sani ko karin bayani a kan kowanne lamari kafin a wallafa ko yadawa," yace.

A halin yanzu, jihar Yobe na da mutum 13 da aka tabbatar suna dauke da muguwar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel