Yadda korona ta kashe dan majalisa a Borno - Iyalansa (Hotuna)

Yadda korona ta kashe dan majalisa a Borno - Iyalansa (Hotuna)

Jauro ya rasu a ranar Talata da ta gabata a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri amma ba a sanar da sanadiyyar mutuwarsa ba.

Amma kuma wata majiya daga iyalansa ta sanar da SaharaReporters cewa ya rasu ne bayan kamuwarsa da muguwar cutar coronavirus.

Yadda korona ta kashe dan majalisa a Borno - Iyalansa (Hotuna)

Yadda korona ta kashe dan majalisa a Borno - Iyalansa (Hotuna). Hoto daga SaharaReporters
Source: Twitter

Majiya daga iyalan marigayi dan majalisar jihar Borno, Umar Audi Jauro, ta yi bayanin yadda dan majalisar ya mutu sakamakon annobar Coronavirus.

Jauro, wanda ya rasu a ranar Talata da ta gabata a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri, ba a bayyana abinda ya yi ajalinsa ba.

Yadda korona ta kashe dan majalisa a Borno - Iyalansa (Hotuna)

Yadda korona ta kashe dan majalisa a Borno - Iyalansa (Hotuna). Hoto daga SaharaReporters
Source: Twitter

Amma kuma wata majiya daga iyalansa a ranar Alhamis ta sanar da SaharaReporters cewa ya rasu ne bayan kamuwa da muguwar cutar coronavirus.

Majiyar ta zargi hukumar asibitin da rashin kula.

Ta ce, "A lokacin da muka garzaya asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri, an ki karbarsa saboda babu gado a cewarsu.

"Sai bayan an karbesa ne aka diba samfur din sa aka mika ga NCDC kuma suka tabbatar yana dauke da cutar bayan mutuwarsa."

Mutuwarsa ta zo ne bayan kwanakin da basu kai bakwai ba da Wakil Bukar, dan majalisa mai wakiltar mazabar Nganzai ya rasu sakamakon cutar korona.

Yadda korona ta kashe dan majalisa a Borno - Iyalansa (Hotuna)

Yadda korona ta kashe dan majalisa a Borno - Iyalansa (Hotuna). Hoto daga SaharaReporters
Source: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: Yadda aka tilasta wa limamai share gidan hakimi a Kano

Yadda korona ta kashe dan majalisa a Borno - Iyalansa (Hotuna)

Yadda korona ta kashe dan majalisa a Borno - Iyalansa (Hotuna). Hoto daga SaharaReporters
Source: Twitter

Yadda korona ta kashe dan majalisa a Borno - Iyalansa (Hotuna)

Yadda korona ta kashe dan majalisa a Borno - Iyalansa (Hotuna). Hoto daga SaharaReporters
Source: Twitter

A wani labari na daban, Wasu limamai a jihar Kano sun shiga hannun jami'an tsaro a karamar hukumar Minjibir bayan an kama su da laifin jan jam'in sallar Juma'a.

An yankewa limaman hukuncin share kofar gidan hakimi har na tsawon wata daya. Kamar yadda kakakin kotunan jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim ya bayyana wa BBC, ya ce baya ga wannan hukuncin an ci su tarar naira dubu goma-goma.

A ranakun karshen makon da ya gabata ne aka kama limaman bayan sun ja dandazon jama'a sallar Juma'a a Masallacin Idi da ke wajen garin Minjibir.

Jibo ya ce kotunan tafi da gidanka 11 gwamnatin jihar Kano ta kirkira don tabbatar da dokar zaman gida.

Daga cikin hukunce-hukuncen da aka taba yi akwai wadanda suka samu bulala saboda karya dokar hana fita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel