COVID-19: Kasashe 5 da korona ta shiga amma ba ta yi kisa ba

COVID-19: Kasashe 5 da korona ta shiga amma ba ta yi kisa ba

An samu bullar cutar a Najeriya ne a watan Fabrairu kuma kawo yanzu (7 ga watan Afrilu) akwai fiye da mutane 3526 da suka kamu da cutar cikinsu 601 sun warke an sallame su yayin da mutum 107 sun mutu.

Kasashen da korona ba ta kashe kowa ba

Duk da cewa annobar ta yadu a kasashe fiye da 180, akwai wasu kasashen da kawo yanzu cutar ba ta kashe kowa ba.

Alkalluma daga Worldometer sun nuna cewa dukkan wadanda suka kamu da cutar a wadannan kasashen sun warke sarai.

Ga jerin kasashen:

1. Falkland Islands

Mutum 13 suka kamu da cutar a kasar kuma dukkansu sun warke

2. Greenland

Cutar ta harbi mutum 11 a Greenland kuma dukkansu sun warke. Greenland ne tsibiri mafi girma a duniya, yana tsakanin tekun Arctic da na Atlantic.

An shafe makonni babu wanda ya sake kamuwa da cutar a kasar bayan mutum 11 suka kamu sun warke.

A ranar 4 ga watan Mayu, gwamnatin kasar ta dage dokar hana fita daga kasar kamar yadda ta bayyana a shafinta na yawon bude ido.

3. Papua New Guinea

Mutum takwas ne suka kamu da cutar a kasar kuma duk sun warke.

A ranar 20 ga watan Maris ne aka samu bullar cutar a kasar daga wani mai hakar maadinai, kwana biyu da samun bullar, gwamnatin PNG ta saka dokar ta baci da hana zirga zirga kamar yadda Guardian ta ruwaito.

4. Saint Barthélemy

Coronavirus ta harbi mutum 6 ne a Saint Barthélemy kuma dukkansu sun warke.

Gwamnatin kasar ta tabbatar da mutum biyu na farko da suka kamu da (COVID-19) a tsibirin na St. Barthélemy a ranar Lahadi 15 ga watan Maris.

An killace dukkan mutanen biyu da suka kamu a gidajensu.

5. Anguilla

Mutum uku ne suka kamu da coronavirus a kasar Anguilla kuma dukkansu sun warke. Kasar ta na nahiyar Amurka ta Arewa.

A watan Afrilu gwamnatin kasar ta dage dukkan takunkumin hana fita waje da yin taro a kasar bayan sanar da cewa babu ko mutum daya mai COVID-19 a kasar.

An dauki wannan matakin ne bayan shugaban likitocin kasar ya shaidawa majalisar zartarwa cewa ana iya janye dokokin hana fita da aka saka kamar yadda wata kafar watsa labarai ta Caribbean Journal ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel