Ke duniya: An damke mutumin da ya birne mahaifiyarsa da ranta

Ke duniya: An damke mutumin da ya birne mahaifiyarsa da ranta

Wata tsohuwar ma'aikaciyar gwamnati wacce ta yi murabus mai suna Wang an birne ta da ranta na kwanaki uku.

Kamar yadda jaridar metro.co.uk ta wallafa, danta mai shekaru 57 ne ya birne ta.

Hukumomi a Jingbian da ke yankin Shaanxi a arewa maso yamma na kasar China sun garzaya inda aka birne matar bayan sun samu rahoto daga sirikar tsohuwar.

An ga yadda jami'an suka fito da tsohuwar mai shekaru 79 daga cikin tabo amma kuma tana numfashi.

A halin yanzu, dan na hannun hukuma inda ake tuhumarsa da yunkurin kisan kai.

Masu bincike sun bayyana cewa ya saka mahaifiyarsa a keken guragu inda ya fitar da ita daga gida wurin karfe 8 na daren Asabar.

Ya dawo gida babu ita a sa'o'in farko na safiyar Lahadi amma ba tare da tsohuwar ba.

Ke duniya: Hukuma ta damke mutumin da ya birne mahaifiyarsa da ranta

Ke duniya: Hukuma ta damke mutumin da ya birne mahaifiyarsa da ranta. Hoto daga jaridar The Punch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Gwamna Tambuwal ya yi babban rashi

A lokacin da matar Zhang ta tambayeshi inda mahaifiyarsa take, Ma ya ce mata ya samu hayar wani matukin mota wanda zai kaita wurin 'yan uwansu.

Ta fara zargin mijin wanda daga bisani ta kai rahoton batan sirikarta mai suna Wang.

Hukumomi sun ce an yi wa dan kiran gaggawa zuwa ofishin 'yan sanda inda ya bayyana cewa ya birne mahaifiyarsa a wani tsohon kabari da ke kudancin garin Jingbian.

Jami'an 'yan sanda sun gano wurin amma abun mamaki sun samu Wang da ranta tana ihun neman taimako don ta dauka kwanaki uku babu abinci ko ruwa.

Har yanzu tana asibiti amma bata cikin matsanancin halin rashin lafiya, hukumomi suka sanar.

A wani labari na daban, hukumar tsaro ta NSCDC reshen jihar Nasarawa ta kama wata mata mai juna biyu mai shekaru 22, Veronica Boniface, saboda kashe mijinta ta hanyar daba masa wuka saboda ya amsa wayar budurwarsa.

Da ake holen wacce ake zargin a hedkwatan hukumar a Lafia, Kwamandan NSCDC a jihar, Habu Fari, ya ce an kama matar ne a garin Obene a karamar hukumar Keana bayan samun bayanan sirri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel