Alkalin da ya soke zaben Abiola na ranar June 12 1993 ya rasu a Bauchi

Alkalin da ya soke zaben Abiola na ranar June 12 1993 ya rasu a Bauchi

Tsohon babban Alkali, Mai Sharia Dahiru Saleh, matawallen masarautar Katagum ya rasu a ranar Alhamis, 7 ga watan Mayu.

Jaridar TheCable ta ruwaito Alkali Dahiru Saleh ya taba zama shugaban babbar kotun babbar birnin tarayya Abuja, ya rasu ne a garin Bauchi, amma za’a yi jana’izarsa a garin Azare.

KU KARANTA: Amfani da Chloroquine: Duk lalube muke yi a cikin duhu – Gwamnan Bauchi

Marigayi Dahiru kuma shi ne Alkalin da ya yanke hukuncin soke zaben shugaban kasa na June 12 1993, zaben da marigayi Cif MKO Abiola yayi ikirarin lashewa a zamanin mulkin Janar IBB.

Alkalin da ya soke zaben Abiola na ranar June 12 1993 ya rasu a Bauchi
Abiola da Dahiru Saleh
Asali: UGC

Masana siyasar Najeriya na ganin ba’a taba yin zaben gaskiya da gaskiya kamar June 12 ba, inda Abiola na jam’iyyar SDP ke kan gaba da Bashir Tofa na jam’iyyar NRC, da tazara mai yawa.

Sai an soke zaben gabanin sanar da sakamakon karshe, wanda hakan ya jefa Najeriya cikin tashin hankali inda jama’a suka fita zanga zanga tare da kira ga shugaban kasa ya sauka.

Matsin lamba ta sa Babangida ya sauka, yayin da ya mika mulki ga Earnest Shonekan, amma ba a dade ba Sani Abacha ya karbe mulkin, daga bisani ya kama Abiola har ya rasu a gidan yari.

A wani labari kuma, Firai ministan kasar Lesotho, Thomas Thabane dan shekara 80 ya nanata aniyarsa ta yin murabus daga mukaminsa a karshen watan Yuli saboda tsufa.

Shugaba Thabane ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 7 ga watan Mayu inda yace watakila ma ba zai kai karshen watan Yuli ba kafin ya jefar da kwallon mangwaro don ya huta da kuda.

Kamfanin dillancin labaru AFP ta ruwaito Thabane ya yi shirin barin mulki ne duk da yiwuwar tuhumarsa da za’ayi sakamakon zarginsa da ake yi da hannu cikin kisan matarsa a 2017.

Kamata yayi Thabane ya sauka a karshen shekarar 2022, wa’adin mulkinsa kenan, amma matsin lamba daga ciki da wajen jam’iyyarsa ta sa zai hakura saboda zarginsa da aikata laifin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel