Tallafin rage nauyin bashi: Buhari ya gana da Firai Ministan Pakistan

Tallafin rage nauyin bashi: Buhari ya gana da Firai Ministan Pakistan

- Shugaba Muhammadu Buhari da takwaransa na kasar Pakistan, Firai Minista Imran Khan, sun gana da juna ta hanyar wayar tarho.

- Tattaunawar shugabannin biyu ta zo ne kwanaki 2 bayan wani taron kungiyar kasashe masu tasowa da shugaba Buhari ya halarta ta hanyar yanar gizo

- Tattaunawar ta gudana ne kan yadda za'a bullo da shirin rage nauyin bashi don taimakawa kasashe masu tasowa a yayin da ake fama da annobar korona a duniya

Ba jimawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da takwaransa na jamhuriyyar Pakistan, Firai Ministan Imran Khan, sun tattauna da juna daga nesa ta hanyar wayar salula.

Fadar shugaban kasa ta bayar da shaidar ganawar shugabannin biyu, a wata sanarwa da ta wallafa kan shafinta na Twitter a ranar Alhamis, 7 ga watan Mayu.

Kamar yadda fadar shugaban kasar ta sanar, ganawar shugabannin biyu ta gudane na kan yadda za'a bullo da shirin rage nauyin bashi don taimakawa kasashe masu tasowa a yayin da ake fama da annobar korona a duniya.

Ana iya tuna cewa, a ranar Litinin, 4 ga watan Mayu, shugaban kasa Buhari ya halarci wani taron kungiyar kasashe masu tasowa ta bidiyon hadi da ake yi ta hanyar yanar gizo.

Shugaban Najeriya; Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya; Muhammadu Buhari
Source: Depositphotos

An gudanar da taron ne domin tumke damarar yaki da cutar korona wadda ta zamo alakakai a duniya.

KARANTA KUMA: Rayuka 1.4m za su salwanta, mutane 6.3m za su kamu da tarin fuka saboda dokar kulle a kan cutar korona - Bincike

Shugaban kasar jamhuriyyar Azerbaijan da ya kasance shugaban kungiyar kasashe masu tasowa, Ilham Aliyev, shi ne ya jagoranci taron mai taken "United Against COVID-19", wato hadin kan yaki da cutar korona.

Daya daga cikin muhimman ababen da suka tattauna shi ne yadda za a bijiro da shirin rage nauyin bashi don taimakawa kasashe masu tasowa wajen yaki da annobar korona da kuma sauran kalubale na durkushewar tattalin arziki da akasarin kasashen ke fuskanta.

Shugaba Ilham wanda ya jagoranci taron, ya yi bayanin cewa kasarsa ta bai wa Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, gudunmuwar dala biliyan 5 a matsayin taimakon yaki da cutar korona.

Ya kuma bayyana cewa kasarsa ta ware dala biliyan 3.5 domin aiwatar da shirye-shiryen bayar da tallafi ga al'umma.

A yayin haka dai ganawar shugaban kasa Buhari da takwansa na Pakistan ta tabo yadda shirin rage nauyin bashi zai tallafawa kasashe masu tasowa yayin da annobar korona ta dugunzuma duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel