COVID-19: Yadda aka tilasta wa limamai share gidan hakimi a Kano

COVID-19: Yadda aka tilasta wa limamai share gidan hakimi a Kano

Wasu limamai a jihar Kano sun shiga hannun jami'an tsaro a karamar hukumar Minjibir bayan an kama su da laifin jan jam'in sallar Juma'a.

An yankewa limaman hukuncin share kofar gidan hakimi har na tsawon wata daya.

Kamar yadda kakakin kotunan jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim ya bayyana wa BBC, ya ce baya ga wannan hukuncin an ci su tarar naira dubu goma-goma.

A ranakun karshen makon da ya gabata ne aka kama limaman bayan sun ja dandazon jama'a sallar Juma'a a Masallacin Idi da ke wajen garin Minjibir.

Jibo ya ce kotunan tafi da gidanka 11 gwamnatin jihar Kano ta kirkira don tabbatar da dokar zaman gida.

Daga cikin hukunce-hukuncen da aka taba yi akwai wadanda suka samu bulala saboda karya dokar hana fita.

COVID-19: Yadda aka tilasta wa limamai share gidan hakimi a Kano
COVID-19: Yadda aka tilasta wa limamai share gidan hakimi a Kano. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kashe-kashe a arewa: Jama'a sun dawo daga rakiyar gwamnati - Gwamnan APC

Mutane da dama an ci tararsu inda wasu aka basu ayyukan yau da kullum da suka hada da share-share.

Gwamna Ganduje da kansa ya kama wasu a kwanar Dan Gora. A cikin motocin akwai manya da suka dauko mutane za su shiga Kano. An ci su tarar N150,000.

A wani labari na daban, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari a jiya Laraba ya ce barazanar rashin tsaro da ke addabar yankin Arewa maso yamma da jihar Katsina ya sa jama'a sun dawo daga rakiyar gwamnati.

A yayin zantawa da shugaban horarwa, Janar Leo Irabor wanda ya kai masa ziyara, ya ce mazauna jihar sun fara kokarin tunkarar 'yan bindigar don hare-haren kullum kara yawaita suke.

"A halin yanzu ina cikin rudani. Ina da kayyadaddun kayan aiki da jami'ai. A tunanina idan aka karfafa jihar nan da kayan aiki da ma'aikata, za mu ga karshen wannan jarabawar," yace.

"Halin da yankin Arewa maso yamma ke ciki abin tashin hankali ne. Annobar Coronavirus ce ke rufe labaran kashe-kashen da 'yan bindiga ke yi a yankunan. A koda yaushe muna cikin barazana ne," yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel