Yanu-yanzu: Almajirai 16 da aka mayar Jigawa daga Kano na dauke da Coronavirus

Yanu-yanzu: Almajirai 16 da aka mayar Jigawa daga Kano na dauke da Coronavirus

Yara Almajirai 16 da gwamnatin jihar Kano ta mayar jihar Jigawa suna dauke da kwayar cutar Coronavirus, gwamnatin Muhammadu Badaru Talamiz, ta sanar.

Kwamishana lafiyan jihar, Abba Zakari, ya bayyana hakan ne a hirar da ya shirya a shafin Facebook dinsa inda yace cikin samfur 45 da aka tura gwaji, 16 na dauke da cutar.

Abba Zakari, wanda shine shugaban kwamitin yakin COVID-19 na jihar ya ce samfurin Almajirai 607 gwamnatin Jigawa ta bada gwaji kuma sakamakon 45 kadai aka samu kawo yanzu.

Tuni an tura Almajiran 16 cibiyar killacewa domin jinyarsu.

Sauran 29 da aka tabbatar ba su dauke da cutar za a mayar da su wajen iyayensu kuma za a baiwa kowanne N10,000 da kayan sawa.

KU KARANTA: Buhari ya nada Alwan Hassan a matsayin mukaddashin shugaban bankin manoma

Kawo karshen Almajiranci

Gwamnoni a Arewacin Najeriya sun lashi takobin kawo karshen Almajiranci a yankin saboda mabarata kawai ake mayar da yara ba tare sun samu ilimin da suka zo nema ba.

Jihohin Arewan sun kaddamar da mayar da Almajirai jihohinsu na asali.

Kawo yanzu, jihar Jigawa ta karbi bakuncin Almajirai 1,114 daga jihar Kano, Kaduna, Gombe da Nasarawa.

Kwamishanan lafiyan Jigawa, Abba Zakari, ya ce yanzu haka suna sauraron Almajirai 99 daga jihar Plateau ranar Alhamis.

Ya ce za a killacesu na tsawo makonni biyu bayan daukan samfurin jininsu.

Amma har yanzu jihar Jigawa bata fara mayar da Almajiran dake cikin jiharta jihohinsu na asali ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel