Kano: Yadda 'yan sanda suka hana dubban mutane shiga Kasuwar Kwari

Kano: Yadda 'yan sanda suka hana dubban mutane shiga Kasuwar Kwari

Jami'an tsaro sun hana dubban yan kasuwa da masu cin kasuwa shiga kasuwar sayar da tufaffi na Kwari da ke Kano a yayin da gwamnatin jihar ta sassauta dokar kulle da ta saka a baya don dakile yaduwar korona.

Idan za a tuna Gwamna Abdullahi Ganduje a makon da ya gabata ya sanar da cewa kasuwannin Yan Kaba da Yan Lemo ne kawai aka bawa damar budewa a ranakun Litinin da Alhamis.

An kuma bawa wasu manyan kantina damar budewa domin sayar wa alumma kayan masarafi a ranakun biyu daga karfe 10 na safe zuwa 4 na yamma.

Kano: Yadda 'yan sanda suka hana dubban mutane shiga Kasuwar Kwari

Kano: Yadda 'yan sanda suka hana dubban mutane shiga Kasuwar Kwari. Hoto daga Daily Trust
Source: UGC

DUBA WANNAN: Katsina: An yanke wa dattijo dan shekara 70 da ya zazzagi Buhari hukunci

An kuma dakatar da yin sallolin Jumaa da zuwa coci a ranakun Lahadi na kimanin sati uku da suka gabata a yunkurin da jihar ke yi na dakile yaduwar annobar ta korona.

A makon da ta gabata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya saka dokar kulle na sati biyu a Kano bayan dokar zaman gida na sati daya da gwamnatin jiha ta saka da farko.

Sai dai wasu shaguna a Kantin Kwari da suke ganin ba su da yadda za suyi suka fita zuwa kasuwar misalin karfe 8 na safe domin bude shagunansu amma yan sanda suka fatattake su.

Daily Trust ta ruwaito cewa wakilinta ya ziyarci kofofi da dama a kasuwar inda ya gano dandazon mutane da suka taho daga kananan hukumomi daban daban domin yin siyayyan bikin sallah a Kano.

Wasu masu shaguna a kasuwar da suka zanta da Daily Trust sun yi kira ga gwamnati ta sake duba dokar hana fitan ta yi sassauci ga masu shaguna a wasu manyan kasuwanin jihar don saukaka wa mutane mawuyacin halin da suka shiga.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel