Coronavirus: Marasa lafiya sun tsere daga wuraren killace wa a jihohin Oyo, Bauchi da Neja

Coronavirus: Marasa lafiya sun tsere daga wuraren killace wa a jihohin Oyo, Bauchi da Neja

Marasa lafiya guda biyu masu cutar korona da ke karbar magani a jihar Oyo da guda daya a jihohin Neja da Bauchi sun tsere daga cibiyoyin killace wa.

An samu masu cutar korona biyu da ake jinyarsu da suka tsere daga cibiyar killace wa a jihar Oyo.

Haka kuma an samu mutum guda a kowane daya daga cikin jihohin Neja da Bauchi da suka kamanta wannan mummunar aika-aika.

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya ce mutane biyu da ke dauke da kwayoyin cutar korona a jihar sun yi layar zana daga cibiyar killace masu jinyar cutar.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, gwamnan ya ce akwai yiwuwar marasa lafiyan gida suka tsere.

Ya ce a halin yanzu mutum 31 cutar korona ta harba a jihar a madadin 33 a sanadiyar mutane biyun da suka arce bayan an tabbatar da sun kamu da cutar.

Makinde ya ba da sanarwar tserewar marasa lafiyan yayin da yake sabunta bayanai a kan alkalumman korona na jihar cikin wani sako da ya wallafa a kan shafinsa na Twitter.

Gwamnan jihar Oyo; Seyi Makinde
Gwamnan jihar Oyo; Seyi Makinde
Asali: Twitter

A cewarsa, "Muna ci gaba da samun karin sakamakon gwajin mutane. An tabbatar da sakamakon wani mutum daya mazaunin Ibadan a ranar 3 ga watan Mayu da ya nuna yana dauke da kwayoyin cutar."

"Sakamakon mutum biyar da ya fito a ranar 4 ga watan Mayu ya tabbata su na dauke da kwayoyin cutar. Hudu daga cikinsu 'yan gudun hijira ne amma daya daga ciki mazaunin Oyo ne."

Sai kuma marasa lafiyar da ta arce a jihar Neja wadda ta kasance mace, ta yi layar zana ne daga cibiyar killace masu cutar da ke garin Minna.

KARANTA KUMA: Coronavirus: 'Ya'yan itatuwa da kayan lambu masu bunkasa garkuwar jiki

Kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Muhammed Makusidi, shi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin ganawa da manema labarai a Minna, babban birnin jihar.

Ya ce matar wadda ta dauko kwayoyin cutar korona tun daga jihar Kano, a yanzu haka ana ci gaba da farautar ta domin dawo da ita cibiyar killace wa.

Babban jami'in gwamnatin ya bayyana damuwa dangane da hatsarin da matar za ta jefa sauran al'umma muddin ta ci gaba da cudanya dasu.

Haka kuma mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Baba Tela, wanda kuma ya kasance shugaban kwamitin kar ta kwana na jihar a kan cutar Lassa da korona, ya tabbatar da layar zana ta daya daga cikin masu cutar korona a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel