Boko Haram: Nakasar da 'yan ta'adda suka samu bayan Buratai ya koma arewa maso gabas

Boko Haram: Nakasar da 'yan ta'adda suka samu bayan Buratai ya koma arewa maso gabas

Hedkwatar tsaro ta kasa tace tsakanin ranar 18 ga watan Maris zuwa 5 ga watan Mayun 2020, rundunar sojin Najeriya ta ga bayan sama da 'yan ta'adda 343 na Boko Haram da ISWAP a yankin Arewa maso gabas din kasar nan.

Shugaban fannin yada labarai na hedkwatar, Manjo Janar John Enenche, ya sanar da hakan ga manema labarai a garin Abuja, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Ya ce da yawa daga cikin 'yan ta'addan sun samu miyagun raunikan wanda da kyar za su tashi yayin da bama-bamai ta sama suka halaka manyan kwamandojin kungiyar ta'addancin.

Enenche ya ce, an tarwatsa tare da lalata da yawa daga cikin makaman 'yan ta'addan kuma an halaka masu musu leken asiri da samar musu da makamai.

Kamar yadda yace, "A cikin wannan halin, wasu daga cikin dakarunmu sun rasa rayukansu yayin da wasu suka samu raunika.

"Dakarunmu sun kwato wasu kauyuka tare da ceto jama'arsu sannan hankula sun kwanta a yankunan.

Boko Haram: Nakasar da 'yan ta'adda suka samu bayan Buratai ya koma arewa maso gabas
Boko Haram: Nakasar da 'yan ta'adda suka samu bayan Buratai ya koma arewa maso gabas. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kashe-kashe a arewa: Jama'a sun dawo daga rakiyar gwamnati - Gwamnan APC

"An samu bayanai tare da bincike mai yawa wanda ya bayyana maboyar 'yan ta'adda da yadda suke gudanar da al'amuransu.

"Ruwan wuta ta jiragen saman yaki duk an yi su wadanda suka tarwatsa kayan yaki da gidajen shugaban kungiyar ta'addancin. An kashe Abu Usamah da kuma wasu mayakansu masu tarin yawa," yace.

A karkashin rundunar Operation Hadarin Daji, Enenche ya bayyana cewa rundunar hadin guiwar ta sojin sama da na kasa tare da jami'an tsaron jihohin Katsina da Zamfara sun samu manyan nasarori.

Ya ce an bankado maboyar 'yan bindiga masu tarin yawa ta hanyar kokarin dakarun. An halaka 'yan bindiga 153 a jihohin Katsina da Zamfara.

Ya kara da cewa, mutum 17 da aka yi garkuwa dasu duk an cetosu tare da mika su ga iyalansu. An samu makamai masu tarin yawa da sauran kayayyaki daga 'yan bindigar.

Kamar yadda yace, dakarun sun kwato shanaye 922 tare da tumaki 446. Ya kara da cewa, sojoji hudu ne suka rasa rayukansu a yayin aiwatar da Operation Whirl Punch.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel