Yadda mota ta murkushe wani mutum yayin da yake wayar bidiyo

Yadda mota ta murkushe wani mutum yayin da yake wayar bidiyo

- Wani mutum ya rasa ransa bayan wata mota kirar Odyssey ta markadeshi a kan babban titin Abeokuta zuwa Sagamu

- Kamar yadda Babatunde Akinbiyi ya bayyana ga manema labarai, mamacin na waya ne amma ta bidiyo yayin da yake tsallaka titi

- motar da mutumin ke ciki ta tsaya ne sakamakon rashin man fetur

Wani mutum wanda har yanzu ba a gano sunanshi ba ya rasa ransa a ranar Laraba.

Wata mota ce kirar Honda Odyssey mai lamba AAA 589 FV ta murkushe shi a kauyen Adedero da ke kan babbar hanyar Abeokuta zuwa Sagamu ga jihar Ogun.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar tabbatar da bin dokokin kan titin, Babatunde Akinbiyi, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai a Abeokuta.

Akinbiyi ya ce lamarin ya faru ne wurin karfe 11 na safe, kamar yadda The Nation ta wallafa.

Ya yi bayanin cewa mamacin wanda namiji ne na yin waya ta bidiyo ne yayin da yake tsallaka titi amma sai mota ta banke shi.

Yadda mota ta murkushe wani mutum yayin da yake wayar bidiyo

Yadda mota ta murkushe wani mutum yayin da yake wayar bidiyo. Hoto daga jaridar Guardian
Source: Original

DUBA WANNAN: COVID-19: Sakamakon gwajin hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya fito

Kamar yadda yace, "An gano cewa motar da mamacin ke ciki mai kirar Mazda na kan hanyarta ta zuwa Abeokuta ne daga Kuto. Direban ya karar da man fetur dinsa ne sai ya tsaya nema.

"Direban ya tsayar da motar a gefen titi don ya samo man fetur yayin da fasinjoji suka sauka don shan iska.

"Amma kuma yayin da mamacin wanda fasinja ne ke dawowa zuwa bakin motar, sai babbar motar ta murkusheshi."

Akinbiyi ya ce gawar mutumin na nan a ma'adanar gawawwaki da ke babban asibitin Ijaiye da ke Abeokuta.

A wani labari na daban, mai taimakawa Shugaba Muhammadu Buhari kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmad ya sanar a shafin Twitter a ranar Laraba cewa an masa gwajin kwayar cutar COVID-19 wato coronavirus kuma baya dauke da cutar.

Ahmad ya bayyana cewa ya shiga wani mawuyacin hali yayin da ake masa gwajin a cikin kwanakin da suka gabata.

Ya bai wa mutane shawara su rika takatsantsan tare da kiyayye dukkan dokoki da shawarwarin da Hukumar kiyayye cuttuka masu yaduwa ta Najeriya, NCDC ke bayarwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel