COVID-19: Masu korona na barazanar komawa gida a Niger (Bidiyo)

COVID-19: Masu korona na barazanar komawa gida a Niger (Bidiyo)

Wasu majinyatan cutar coronavirus da ke killace a cibiyar killacewa a garin Minna, jihar Neja sun yi barazanar sallamar kansu a kan yadda ake nuna musu halin-ko-in-kula.

A wani bidiyo da SaharaReporters ta gani a ranar Laraba, wasu daga cikin majinyatan sun nuna tsananin fushinsu a kan halin da suke ciki. Sun ce yadda ake ciyar dasu bai gamsar dasu ba.

Sun bukaci a barsu a gidajensu a maimakon a killacesu yunwa ta halaka su.

A halin yanzu, hankali ya kasa kwanciya a jihar bayan wata mata ta tsere daga cibiyar killacewa ta jihar.

A bidiyon, an ji majinyatan suna ta maganganu a kan rasin kulawar da shugabanni ke nuna musu yayin da suke jinyar.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Dan majalisa a jihar Yobe ya kamu da cutar Korona

A wani labarin na daban, dan majalisar jihar Yobe, Lawan Nguru ya kamu da cutar COVID-19, ya sanar da hakan a ranar Laraba.

Dan majalisar ne ke wakiltar mazabar Nguru kuma shi kadai ne daga jam'iyyar adawa ta PDP a majalisar, kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.

A wata takarda da ta fito daga dan majalisar a garin Damaturu, ya ce ya killace kansa kamar yadda masana kiwon lafiya suka sanar.

Amma kuma, ya musanta rahoton cewa ya ki killace kansa. Ya jaddada cewa ba zai taba yin zagon kasa ga kokarin gwamnatin jihar na shawo kan annobar tare da saka rayukan jama'a a hatsari ba.

Ya bayyana tabbacin cewa yadda gwamnatin jihar Yobe ke daukar mataki a kan cutar, za a shawo kan annobar.

Ya shawarci jama'ar jihar da su kiyaye shawarwarin masana kiwon lafiya wajen hana yaduwar cutar.

Nguru ya ce: "A halin yanzu, ina cibiyar killacewa kuma ina samun saukin halin da nake ciki. Ina jiran umarnin likitoci.

"Ina sake jinjina ga gwamnatin jihar Yobe a kan yadda take kula da mu masu jinyar jihar da kuma kokarin hana yaduwar cutar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel