Ma'aikatan jinya 18 sun kamu da korona a Kano

Ma'aikatan jinya 18 sun kamu da korona a Kano

- A kalla malaman jinya 18 ne suka kamu da cutar Korona a jihar Kano, kungiyar ma'aikatan jinya da ungo-zoma ta kasa ta tabbatar

- Kamar yadda Kwamared Ibrahim Muhammad ya sanar, an dauka samfur din ma'aikatan jinya 86 amma an tabbatar da 18 na dauke da cutar

- Shugaban ya yi bayanin cewa, tara daga cikin ma'aikatan jinya na aiki da asibitin kashi na Dala yayin da bakwai ke aiki da AKTH

A kalla ma'aikatan jinya 18 ne suka kamu da cutar korona a jihar Kano.

Shugaban kungiyar ma'aikatan jinya da ungu-zoma ta kasa a reshen jihar Kano, Kwamared Ibrahim Muhammad ne ya sanar da hakan.

Ma'aikatan jinya 18 sun kamu da korona a Kano

Ma'aikatan jinya 18 sun kamu da korona a Kano. Hoto daga Vanguard
Source: UGC

DUBA WANNAN: Katsina: An yanke wa dattijo dan shekara 70 da ya zazzagi Buhari hukunci

Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, ya ce 18 daga cikin samfur 86 da aka kai na ma'aikatan jinyar ya bayyana cewa suna dauke da cutar.

Ya yi bayanin cewa tara daga ciki duk ma'aikata ne a asibitin kashi na Dala. Ragowar bakwai daga ciki kuwa ma'aikata ne a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.

Rahoton ta bayyana cewa likitoci 34 ne a jihar Kano suka kamu da cutar kamar yadda shugaban kungiyar likitoci, Dr Sanusi Bala ya bayyana.

Muhammad ya yi kira ga gwamnati da ta samar da kayayyakin kariya garesu don su sauke nauyin da ke kansu.

A wani rahoton, mun kawo muku cewa Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta aike da tawagar masu bayar da taimakon gaggawa, RRT, zuwa Kano domin tallafawa gwamnatin jihar dakile yaduwar COVID-19.

Hukumar ta bayyana hakan ne a ranar Laraba cikin sanarwar da ta fitar inda ta ce hakan ya zama dole ne domin dakile yaduwar cutar a jihar cikin gaggawa.

Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, ta ruwaito cewa an samu bullar cutar a jihar a ranar 11 ga watan Afrilu ne amma a yanzu adadin wadanda suka kamu sun kai 342 kuma cutar ta kashe mutum takwas.

A yunkurin ta na dakile yaduwar cutar, WHO ta sake aike wa da sabbin jami'ai masu sanya idanu 88 zuwa kananan hukumomi 44 da ke jihar.

A cewar WHO, jami'ai masu sanya idanun za su taimaka wurin kai rahoto game da wadanda ke da cutar da nemo wadanda suka yi cudanya da masu cutar da dakile yaduwar ta.

Jagoran tawagar WHO a jihar, Dr Jibrin Alkasim ya ce karuwar wadanda ke dauke da cutar a jihar ya sa dole a binciko wadanda suka yi cudanya da wanda aka gano suna da cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel