Yanzu-yanzu: Sabbin mutane 195 sun kamu da Coronavirus; Legas, Kano, Zamfara da Sokoto kekan gaba

Yanzu-yanzu: Sabbin mutane 195 sun kamu da Coronavirus; Legas, Kano, Zamfara da Sokoto kekan gaba

Cibiyar hana yaduwar cututtuka a Najeriya watau NCDC ta sanar da samun karin mutane 195 da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Laraba, 6 ga Mayu, 2020.

Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: An samu karin mutane dari da tis'in da biyar (195) sun kamu da #COVID19. Yayinda 53 suka samu waraka, 5 sun mutu.

82-Lagos, 30-Kano, 19-Zamfara, 18-Sokoto, 10-Borno, 9-FCT, 8-Oyo, 5-Kebbi, 5-Gombe, 4-Ogun, 3 Katsina, 1-Kaduna, 1-Adamawa.

Jimilla:

Kamuwa: 3145

Sallama: 534

Mutuwa: 103

KU KARANTA: Matawalle ya nada madadin marigayi Sarkin Kauran Namoda

A yayin da likafar annobar korona ke ci gaba babu sassauci, wata kungiyar masu bincike a Jami'ar Fasaha ta Akure da ke jihar Ondo, ta yi wani bincike kan muhimmancin ta'ammali da wasu 'ya'yan itatuwa da kayan lambu masu bunkasa garkuwar jiki.

Sanadiyar yadda kawo yanzu ba a samar da maganin cutar korona ba, a halin yanzu dai ingatacciyar garkuwar jiki ita kadai ce ke iya yakar cutar a jikin mutum kamar yadda mahukuntan lafiya suka bayyana.

Kwararrun masanan na jami'ar FUTA sun bayar da sharawa a kan muhimmancin bunkasa garkuwa jiki ta hanyar ci da kuma shan wasu dangin 'ya'yan itatuwa da kayan lambu masu tarin sunadarai.

Jagoran masu binciken da ya kasance kwararren masani a fannin kimiya da fasahar abinci, Farfesa Ganiyu Oboh, ya ce kayan lambu da 'ya'yan itatuwa sun kunshi sunadarai masu bunkasa garkuwar jiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel