Buhari ya yi ma mai martaba Sarkin Daura addu’ar samun lafiya

Buhari ya yi ma mai martaba Sarkin Daura addu’ar samun lafiya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika da sakon fatan alheri ga mai martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Farouk Umar biyo bayan kwantar da shi da aka yi a asibiti.

A yan kwanakin nan ne aka kwantar da Sarkin Daura Farouk a cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya dake garin Katsina sakamakon wata rashin lafiya da ta rutsa da shi.

KU KARANTA: Ministan Buhari, Raji Fashola ya bayyana matakin da yake dauka na kariya daga Coronavirus

Buhari ya fitar da sanarwar ta bakin kakaakinsa, Garba Shehu, inda yace a matsayinsa na Bayajiddan Daura, ya kadu da samun labarin rashin lafiyar Sarkin, don haka yana masa addua.

“Ina tare da kafatanin al’ummar masarautar Daura da ilahirin jama’an jahar Katsina wajen yi ma Sarkinmu Alhaji Farouk Umar Farouk addu’an samun sauki tare da fatan alheri a gare ka.” Inji shi.

Daga karshe shugaba Buhari yace ya ji dadin rahoton da yake samu game da cigaban da Sarkin yake samu a lafiyarsa.

Buhari ya yi ma mai martaba Sarkin Daura addu’ar samun lafiya
Sarkin Daura Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Idan za’a tuna, gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana dalilin da yasa gwamnati ta dauki matakin garkame fadar masarautar Daura a karshen makon da ta gabata.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin da ganawa da manema labaru, inda yace suna fargabar samun bullar Coronavirus a fadar ne shi yasa suka garkame ta.

“Fadar masarauta, kamar gidan gwamnati ne, wuri ne dake cike da mutane da dama, don haka muka yanke shawarar kula da lamarin ta hanyar yi ma mazauna fadar gwaji, a haka mun yi ma mutane 89 gwaji.

“A yanzu dai muna jiran samun sakamakon gwajin nasu, daga nan zamu san mataki na gaba da zamu dauka, shi yasa kaga muka mamaye fadar kamar yadda Sojoji suke yin juyin mulki, ta haka ne kadai zamu iya gane wadanda ke dauke da cutar a fadar.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel