COVID-19: Sakamakon gwajin hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya fito

COVID-19: Sakamakon gwajin hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya fito

Mai taimakawa Shugaba Muhammadu Buhari kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmad ya sanar a shafin Twitter a ranar Laraba cewa an masa gwajin kwayar cutar COVID-19 wato coronavirus kuma baya dauke da cutar.

Ahmad ya bayyana cewa ya shiga wani mawuyacin hali yayin da ake masa gwajin a cikin kwanakin da suka gabata.

Ya bai wa mutane shawara su rika takatsantsan tare da kiyayye dukkan dokoki da shawarwarin da Hukumar kiyayye cuttuka masu yaduwa ta Najeriya, NCDC ke bayarwa.

DUBA WANNAN: Katsina: An yanke wa dattijo dan shekara 70 da ya zazzagi Buhari hukunci

Ya shawarci mutane su cigaba da hakuri har zuwa lokacin da lamura za su koma yadda suke a baya.

Ga dai sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

"Cikin yan kwanakin da suka shude an min gwajin COVID–19 , tabbas abin babu dadi ko kadan. Don Allah ku rika takatsantsan da kiyayye kanku.

"Ku rika bin shawarwarin da hukumar NCDC ke bayarwa har zuwa lokacin da abubuwa za su daidaita saboda kada a muku irin gwajin da aka yi min.

"Nagode wa Allah, sakamakon gwajin ya nuna bana dauke da kwayar cutar."

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Tanzania, John Magufuli ya bayyana damuwarsa game da naurorin gwajin kwayar cutar COVID-19 da aka sayarwa kasarsa bayan an yi wa gwanda da akuya gwajin kuma sakamakon ya nuna sun kamu da corona.

A cewar Aljazeera, Magafuli, wanda ya yi jawabi a ranar Lahadi a wani taro a Chato, arewa maso yammacin kasarsa ya ce ya umurci a fara bincike a kan ingancin naurar gwajin.

An ruwaito cewa sun dauki samfurin gwaji daga wasu ababen da ba dan adam ba kamar akuya, tinkiya da gwanda.

Sannan aka saka wa samfurin sunayen mutane da shekaru aka tura wa dakin gwajin kwayar cutar da corona da ke kasar domin ayi gwajin ba tare da masu gwajin sun san ainihin inda aka debo samfurin ba.

Daga bisani sakamakon ya nuna akuya da gwanda sun kamu da cutar.

Magufuli ya bayar da umurnin gudanar da sahihin bincike game da lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel