Macen-macen Jigawa: Shugaban karamar hukuma ya yi karin bayani

Macen-macen Jigawa: Shugaban karamar hukuma ya yi karin bayani

Shugaban karamar hukumar Hadejia ta jihar Jigawa, Alhaji Abdullahi Maikanta a ranar Laraba ya ce mace-macen da ake fuskanta a jihar bashi da alaka da COVID-19.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa an yi mace-macen daga ranar 30 ga watan Afirilu zuwa 6 ga watan Mayu.

Maikanti ya ce mutum uku ne kacal suka rasa rayukansu a wannan lokacin ba kamar yadda kafafen yada labarai ke cewa 100 ba.

Shugaban karamar hukumar ya ce a ranar Talata ne aka tabbatar da mutuwar rayuka 47 a yankin.

Maikanti ya sanar da NAN cewa, wadanda suka mutun yawanci manyan mutane ne masu ciwuka daban-daban.

"Bayan binciken da muka yi tare da tattaunawa da iyalan mamatan, mun binciki asibitin Gawuna da kuma makabartu amma mun gano cewa rayuka 47 ne aka rasa daga ranar 30 ga watan Afirilu zuwa 6 ga watan Mayu.

Macen-macen Jigawa: Shugaban karamar hukuma ya yi karin bayani
Macen-macen Jigawa: Shugaban karamar hukuma ya yi karin bayani. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zanga-zangar rashin abinci: Mun shawo kan matsalar majinyatan -Gwamnati

"Mamatan duk tsofaffi ne masu shekaru daga 70 zuwa 100. Tuni dama suna fama da ciwuka irinsu hawan jini, asma da shanyewar bangaren jiki na dogon lokaci.

"A iyakar bincikenmu, babu mamacin da muka ga ya bayyana da wata alama ta COVID-19," yace.

A kan gujewa kamuwa da annobar, shugaban karamar ya ce a cikin kwanakin nan ne suka kama wasu motoci uku dauke da 'yan kasuwa a yankin.

"Da yawa daga cikinsu sun zo ne daga jihohin Bayelsa da Binuwai don siyan kwadi a kasuwanninmu.

"Tsoronmu shine kada mutanen nan su kwaso mana kwayar cutar kuma su goga wa wasu a kasuwannin.

"Amma daga bisani mun saki ababen hawansu bayan sun dauka alkawari a rubuce cewa za su kiyayi kasuwanninmu," Maikanti yace.

Ya ce karamar hukumar ta mayar da hankali wurin wayar da kai ga mazauna yankin a kan amfanin nisantar juna, wanke hannaye da kuma yadda ake tari.

A jiya ne wani labari ya bayyana cewa an samu a kalla mace-macen mutum 100 a jihar Jigawa cikin kwanaki kalilan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel