Asusun Bayar da Lamuni ya danka wa Najeriya tallafin gaggawa na $3.4bn

Asusun Bayar da Lamuni ya danka wa Najeriya tallafin gaggawa na $3.4bn

Rahotanni sun bayyana cewa, Asusun Bayar da Lamuni na Duniya IMF, ya danka wa Najeriya tallafin gaggawa na dalar Amurka biliyan 3.4.

Asusun lamunin ya amince da baiwa gwamnatin Najeriya tallafin $3.4bn (N1.2 tiriliyan) domin ceto tattalin arzikin kasar sanadiyar barkewar muguwar cuta mai sarkewar numfashi ta korona.

Tun a ranar Talata 28 ga watan Afrilu, kwamitin zartarwa na Asusun Lamunin ya amince da bukatar gwamnatin Najeriya bayan da ta nemi tallafin kudin har dala biliyan 3.4.

Shugabar Asusun, Kristalina Georgieva, ita ce ta sanar da hakan yayin ganawa da kamfanin dillancin labarai na CNBC Africa a ranar Talata.

Georgieva ta ce an shigar da wannan tarin kudi cikin asusun ajiyar gwamnatin Najeriya da ke babban bankin kasar.

Asusun lamunin da yake bada tallafin mai suna 'Rapid Financing Instrument (RFI)' ga kasashe masu rajista da asusun, duk da cewa kasashen babu su a cikin kowane irin shirin taimako da ya ke bayar wa.

Sabanin yadda wasu ke hange, ko kadan wannan kudi da Najeriya ta karba ba rance bane.

Tsarin gudanarwa na IMF ya bai wa wasu kasashe damar ajiye wani kaso na lalitar dukiyarsu a Asusun.

Shugaba ta Asusun Bayar da Lamuni na Duniya; Kristalina Georgieva
Shugaba ta Asusun Bayar da Lamuni na Duniya; Kristalina Georgieva
Asali: Depositphotos

Ana rike wadannan ajiya cikin kudin da ake kira SDR (hakkin zarar kudi na musamman).

Darajar SDR ta dogara ne a kan darajar kudin wasu kasashen duniya ciki har da na Amurka, Turai, Birtaniya, Japan da kuma na kasar Sin.

KARANTA KUMA: Coronavirus: Najeriya za ta debo 'yan kasarta daga kasashen ketare

Dala biliyan 3.4 da Najeriya ta samu a yanzu yana wakiltar SDR 2,454.5 miliyan kenan, kaso 100% na adadin kudin da Najeriya ke rike da su a IMF

Sai dai IMF na bari kasashe su zari wannan kudi domin saduwa da bukatun gaggawa kama daga aukuwar bala'o'i, barkewar rikici, tashin farashin kayayyaki da kuma sauran bukatu yayin da kasa ta fuskanci rauni.

Kasancewarta mamba a IMF, dole ne Najeriya ta sake dawo da wannan ajiya cikin asusun na IMF.

Haka kuma dole ne Najeriya ta sake gina wannan ajiyar a Asusun Lamunin cikin lokacin da bai wuce shekaru 3 zuwa 5 ba.

IMF na bayar da irin wannan tallafi ga kasashen da su ke fuskantar matsalolin kudi.

A cikin sanarwar bayar da lamunin da ya fitar, IMF ya ce a shirye ya ke ya bayar da shawarwari kan manufofin yadda Najeriya za ta batar da wannan kudi.

IMF ya kuma bukaci gwamnatin Najeriya da ta kwatanta gaskiya wajen bayyana duk wani shige da fice da za ta yi yayin kashe kudaden.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel