Baku isa ku fadawa Buhari abinda zai yi ba - Mai magana da yawunsa

Baku isa ku fadawa Buhari abinda zai yi ba - Mai magana da yawunsa

Yan Najeriya sun yi ca kan mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, a kafafen raayi da sada zumunta kan maganar isgilin da ya yiwa wani yan Najeriya.

Ya yi wannan katobara ne yayinda ya caccaki wani dan Najeriya da ya bukaci maigidansa shugaba Buhari yayi hira kai tsaye da manema labarai.

Za ku tuna cewa tun da Buhari ya hau mulki a 2015, sau daya ya taba hira da manema labarai kai tsaye, sabanin abinda sauran takwarorinsa na kasashen duniya ke yi kusan kulli yaumin.

Wani mutumi mai suna, Ibikunle, yayin wata hira a gidan rediyon Nigeria Info ya bukaci Femi Adesina ya ja hankalin Buhari ya fito yayi hira da manema labarai.

A martaninsa, Femi Adesina, ya caccaki mutumin inda yace kada mutane suyi tunanin dan sun zabi shugaban kasa za su iya juyashi yadda suka ga dama.

Yace “Lokacin da wannan annobar ta COVID ta fara, (mutane na faman cewa) shugaban kasa yayi mana magana, (amma) yanzu ya yi magana har sau uku, me kuma kuke so?“

“Mutane suna tunanin don sun zabi shugaban kasa ko basu zabeshi ba, sai sun fada masa abinda zai yi. Ba zai yiwu ba.“

“Don ku zabi mutun kawai sai ku rika juyashi yadda kuka ga dama. Shugaban kasa zai yi duk abinda ya ga maslaha ne ga alumma a ko wani lokaci.“

KU KARANTA An yanke wa wani mutum hukuncin kisa ta yanar gizo a Najeriya

A wani labarin daban, Wata kotu da ke zamanta a jihar Katsina a ranar Talata ya yanke wa wani mutum mai shekaru 70, Lawal Abdullahi Izala, hukuncin daurin watanni 18 a gidan gyaran hali.

An kama Izala ne a makon da ta gabata a kan zarginsa da zagin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

An gurfanar da dattijon da wasu mutane biyu a gaban kuliya a kan tuhumar furta kalaman da ka iya tayar da zaune tsaye da kuma rashin yi wa hukuma da a ta hanyar furta maganganu na cin mutunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel