COVID-19: 'Yar shekaru 6 ta kamu da cutar Korona a Jigawa

COVID-19: 'Yar shekaru 6 ta kamu da cutar Korona a Jigawa

Yarinya mai shekaru shida wacce take diya ga mutum na farko da ya kamu da cutar korona a karamar hukumar Kazaure ta jihar Jigawa ta kamu da cutar.

Kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa, kwamishinan lafiya na jihar kuma shugaban kwamitin yaki da cutar na jihar, Dr Abba Zakari, ya bayyana hakan a garin Dutse, babban birnin jihar.

Kamar yadda kwamishinan ya bayyana, an dauka samfur din mutum 18 wadanda aka gano sun yi mu'amala da mutum na farko da ya kamu da cutar a jihar. Na yarinyar ne kadai ya bayyana tana dauke da cutar.

Ya ce babu dadewa za a kai yarinyar cibiyar killacewa ta jihar inda mahaifinta yake.

Hakan ne ya kai jimillar masu cutar a jihar zuwa 32.

Kamar yadda jaridar The Punch ta bayyana, mutum 72 ne a halin yanzu ke dauke da kwayar cutar a jihar.

COVID-19: 'Yar shekaru 6 ta kamu da cutar Korona a Jigawa
COVID-19: 'Yar shekaru 6 ta kamu da cutar Korona a Jigawa. Hoto daga jaridar Blueprint
Asali: UGC

KU KARANTA: Zanga-zangar rashin abinci: Mun shawo kan matsalar majinyatan -Gwamnati

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Bauchi ta ce ta shawo kan matsalar rashin ciyarwa da majinyatan COVID-19 ke fuskanta a cibiyar killacewa ta jihar.

Wani mutum mai suna Buhari Tafida, wanda ya yi ikirarin shi majinyaci ne a asibitin koyarwa na jami'ar Abubukar Tafawa Balewa ya wallafa cewa ba a basu abinci har sai karfe 8 na dare a shafinsa na Twitter.

A wata takarda da Lawal Mu'azu, mai bada shawara na musamman ga gwamnan a kan yada labarai ya fitar, ya ce wannan jinkirin da suka yi na kaiwa majinyatan abinci ba da gangan bane.

"Hankalin gwamnatin jihar Bauchi ya kai ga koken da majinyatan COVID-19 ke yi na cewa ba a kai musu abinci da wuri. Tuni gwamnatin ta dauka matakin shawo kan matsalar a take," yace.

"Jinkirin kai musu abincin da aka yi ba da gangan bane kuma an yi dana-sani. Daya daga cikin majinyatan ya tabbatar da cewa an shawo kan matsalar kuma sun samun kular da ta dace.

"Gwamnatin jihar Bauchi ta dauka alkawarin duba duk wani kalubale da zai sa ta inganta jin dadin jama'ar jihar ballantana masu fama da muguwar cutar.

"Duk da karuwar yawan masu cutar da ake samu a jihar, gwamnatin jihar za ta yi kokarin ganin ta shawo kan yaduwar cutar a jihar," ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel