Yadda aka yi wa kwarto dukan kisa

Yadda aka yi wa kwarto dukan kisa

- 'Yan kungiyar asiri sun yi wa wani mutum mai suna Timothy Osai mugun dukan da ya kashe shi a karamar hukumar Ohaji-Egbema ta jihar

- Bayan an zarga mamacin da kwartanci da matar wani basarake a yankin, dan uwansa ya ja mishi kunne amma bai ji ba

- Bayan miyagun raunika sun yi ajalin Osai, fusatattun matasan yankin sun bankawa gidaje shida wuta don nuna damuwarsu

Wani mutum mai suna Timothy Osai mai shekaru 34 ya sha mugun duka wanda ya yi sanadin mutuwarsa.

Ana zargin Osai ne da kwartanci da matar wani mai sarauta a Ihie, karamar hukumar Ohaji-Egbema da ke jihar Imo, jaridar The Nation ta wallafa.

An gano cewa wadanda suka kashe shi din hayarsu aka yi, kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.

Osai ya mutu ne sakamakon raunikan da ya samu bayan ya sha muguwar jibga.

Lamarin ya faru ne a ranakun karshen makon da suka gabata.

An gano cewa Osai na mu'amala da matar auren wacce dan uwan shi ya ja masa kunne a kan hakan.

Bai ji jan kunnen ba, lamarin da yasa aka kira mishi 'yan kungiyar sirri wadanda suka aika shi lahira.

Yadda aka yi wa kwarto dukan kisa
Yadda aka yi wa kwarto dukan kisa
Asali: Facebook

KU KARANTA: COVID-19: An kwantar da Sarkin Daura a asibiti, yana ICU

Mutuwar Osai ta sa fusatattun matasa sun banka wa gidaje shida gobara don zanga-zanga a kan abinda 'yan kungiyar asirin suka yi.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Orlando Ikeokwu bai tabbatar da aukuwar lamarin a yayin rubuta rahoton nan ba.

A wani labari na daban, an kwantar da Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar a sashen kula ta musamman ta asibitin tarayya da ke jihar Katsina.

Daura ce garin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wata majiya daga fada a ranar Talata ta ce an gaggauta mika Umar asibiti a daren Litinin kuma an kwantar da shi sakamakon mawuyacin halin da yake ciki.

Ana zargin Umar ya kwashi cutar COVID-19 daga likitan jihar Katsina, Dr Aminu Yakubu, wanda ya rasu sakamakon cutar a watan da ya gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: