Allah ya yi wa Kilishin Katsina, Alhaji Iro Sabe rasuwa

Allah ya yi wa Kilishin Katsina, Alhaji Iro Sabe rasuwa

A jiya ne aka birne gawar Alhaji Iro Sabe, Kilishin Katsina a makabartar Dan Tukum bayan an yi jana'izarsa a Kofar Soro.

Babban limamin jihar Katsina, Liman Muddaha ne ya ja sallar gawar inda ya yi addu'ar rahama ga mamacin da kuma fatan juriyar rashin ga iyalansa.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa, marigayin ya rasu yana da shekaru 75 kuma ya bar mata biyu da 'ya'ya 20 tare da jikoki masu tarin yawa.

Daga cikin 'ya'yansa akwai Mannir Iro Sabe, dan kasuwa, Audu Sabe, ma'aikaci da hukumar kwastam, Bishir Sabe, ma'aikacin kotu da Dr Bashir Sabe, malami a jami'ar Umaru Musa da ke Katsina.

Allah ya yi wa Kilishin Katsina, Alhaji Iro Sabe rasuwa

Allah ya yi wa Kilishin Katsina, Alhaji Iro Sabe rasuwa
Source: Twitter

KU KARANTA: Boko Haram: Dakarun Nijar sun yi wa 'yan ta'adda ruwan wuta

A wani labari na daban, An kwantar da Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar a sashen kula ta musamman ta asibitin tarayya da ke jihar Katsina. Daura ce garin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wata majiya daga fada a ranar Talata ta ce an gaggauta mika Umar asibiti a daren Litinin kuma an kwantar da shi sakamakon mawuyacin halin da yake ciki.

Ana zargin Umar ya kwashi cutar COVID-19 daga likitan jihar Katsina, Dr Aminu Yakubu, wanda ya rasu sakamakon cutar a watan da ya gabata.

Matar sarkin Daura, Hajiya Binta Umar Farouk ta rasu a makonni biyu da suka gabata.

"A daren jiya ne aka hanzarta mika sarkin Daura asibitin tarayya da ke Katsina. A halin yanzu, an umarcemu da mu killace kanmu.

"Likitan da cutar ta kashe a jihar ya yi mu'amala da sarkin Daura da matarsa wacce ta rasu. Likitan ne ke duba lafiyar basaraken da matarsa.

"An umarci sarkin da ya killace kansa tun bayan mutuwar likitan amma bai saurara hakan ba. Ya bari ana shige da fice a fadar," majiyar ta sanar da SaharaReporters.

A ranar Litinin ne Dr Mustapha Inuwa, sakataren gwamnatin jihar Katsina yace an samu wasu masu dauke da cutar a fadar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel