Labari mai dadi: Manyan yan kasuwan Kano sun amince da rage farashin kayan abinci

Labari mai dadi: Manyan yan kasuwan Kano sun amince da rage farashin kayan abinci

Kungiyar manyan yan kasuwan Singer ta jahar Kano sun dauki alkawarin rage farashin kayan masarufi domin taimaka ma al’ummar jahar.

Hukumar karbar koke koke da yaki da rashawa ta jahar Kano, PCACC, ce ta sanar da haka a ranar Talata, inda ta ce yan kasuwan sun dauki wannan alkawari ne bayan sun gana da ita.

KU KARANTA: Za’a gudanar da gwajin COVID-19 a kan yan kwallon Barcelona kafin La Liga ta cigaba

“An cimma yarjejeniya tsakanin PCACC da yan kasuwar Singer kan cewa daga yanzu farashin buhun siga ya koma N16,000, kuma farashin dukkanin kayan abinci zai koma kamar yadda yake a da.

“Amma ban da shinkafa, saboda sun ce a yanzu basu da shi a kasa, don haka hukumar za ta shirya ganawa da kungiyar masu sarrafa shinkafa a jahar don kula da rawar da suke takawa wajen tsawwala farashin shinkafar.” Inji hukumar.

PCACC ta yi wannan hubbasa ne sakamakon kiraye kirayen jama’a a gareta da kuma korafe korafe game da hauhawar farashin kayan abinci, don haka ta tashi tsaye don share musu kuka.

PCACC ta ce ta yi amfani da sashi na 9 da na 15 na dokokin ta da suka bata ikon kaddamar da binciken korafe korafe, da haka ta gano wasu wurare da ake taskance kayan abinci.

Ta kama buhuna 19, 500 na fulawa, kwalin taliya 79,645, buhunan siga 5,120 da taliyar macaroni kwali 37,000, kuma za ta gurfanar da su gaban kotu da zarar ta kammala gudanar da bincike.

Wannan tasa hukumar ta sake yin zama tare da shuwagabannin kasuwar a karkashin jagorancin Alhaji Uba Zubair Yakubu inda suka amince da yarjejeniya kamar haka;

- Za su mayar da farashin siga zuwa N18,000 daga ranar 4 ga watan Mayun 2020.

- Tsadar farashin ya biyo karancin kayan ne a kasuwa sakamakon kamfanoni sun ki sako musu kaya, don haka hukumar ta amince da yi ma gwamna magana domin ya gana da kamfanonin da yan kasuwan

- Kasuwar Singer za ta raba kayan masarufi ga shaguna da manyan kantuna a jahar

- Hukumar za ta saki kayan da ta kama, kuma za’a raba su a Singer, shaguna da manyan kantuna

- Yan kasuwan sun amince idan aka bude kasuwar na tsawon kwanaki 3, farashin kaya zai sauka

- Dole a dabbaka tsarin tsayawa nesa nesa da juna a kasuwar Singer da manyan kantuna

- Idan yarjejeniyar da aka dauka ya tabbata, farashin siga zai koma N16,000

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel