Katsina: An yanke wa dattijo dan shekara 70 da ya zazzagi Buhari hukunci

Katsina: An yanke wa dattijo dan shekara 70 da ya zazzagi Buhari hukunci

Wata kotu da ke zamanta a jihar Katsina a ranar Talata ya yanke wa wani mutum mai shekaru 70, Lawal Abdullahi Izala, hukuncin daurin watanni 18 a gidan gyaran hali.

An kama Izala ne a makon da ta gabata a kan zarginsa da zagin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

An gurfanar da dattijon da wasu mutane biyu a gaban kuliya a kan tuhumar furta kalaman da ka iya tayar da zaune tsaye da kuma rashin yi wa hukuma da a ta hanyar furta maganganu na cin mutunci.

Katsina: Kotu ta yanke wa dattijo dan shekara 70 da ya zazzagi Buhari hukunci
Katsina: Kotu ta yanke wa dattijo dan shekara 70 da ya zazzagi Buhari hukunci. Hoto daga Westafco
Asali: UGC

Da ya ke magana da manema labarai a ranar Talata, Izala ya ce ya yi furucin ne a cikin fushi lokacin da ya ziyarci kauyensu ya gano cewa yan bindiga sun kashe wasu yan uwansa sun kuma sace shanu 15.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Dan majalisar jihar Borno ya rasu a asibiti

A yayin zartar da hukuncin, alkalin kotun ya ce an samu Izala da laifuka biyu na assasa fitina da rashin daa ga hukuma.

An yanke masa hukuncin daurin watanni shida a gidan gyaran hali na laifin farko sai kuma na shekara guda na laifi na biyu.

Sai dai an bawa Izala zabin biyan tara ta ₦10,000 na laifin farkon da kuma ₦20,000 na laifin na biyu.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa wasu mutane masu tausayi a jihar sun biya wa dattijon kudin tarar da aka ci shi na ₦30,000.

An kuma saki dattijon ya koma gidansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel