Yanzu-yanzu: Dan majalisar jihar Borno ya rasu a asibiti

Yanzu-yanzu: Dan majalisar jihar Borno ya rasu a asibiti

Dan majalisar Borno mai wakiltar mazabar Bayo a majalisar jihar, Umar Audi ya rasu.

Ya rasu ne a Asibitin Koyarwa ta Jamiar Maiduguri a yammacin ranar Talata kamar yadda The Cable ta ruwaito.

An ce ma'aikatan lafiya a asibitin sun dage cewa babu gadon da za a bashi inda suka ce gadon kawai da ya rage na mata masu haihuwa ne.

Amma iyalansa da suka kai shi asibitin sunyi kokarin shawo kan ma'aikatan asibitin inda daga bisani suka karbe shi.

Yanzu-yanzu: Dan majalisar jihar Borno ya rasu a asibiti
Yanzu-yanzu: Dan majalisar jihar Borno ya rasu a asibiti
Asali: Original

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa Sarkin Kauran Namoda rasuwa

Majiyar ta ce, "Ya mutu jim kadan bayan an bashi gado. An dauki samfuri daga jikinsa an aike wa Hukumar kiyayye cututtuka masu yaduwa, NCDC, domin a tabbatar idan mutuwarsa na da alaka da COVID-19.”

A wani labari mai kama wa da wannan, kun ji cewa Allah ya yi wa Kakah Hajja, mahaifiyar babban hafsin sojojin Najeriya rasuwa a ranar Talata.

Wata majiya daga dangin su Buratai ya shaida wa Sahara Reporters cewa marigayiya Hajja ta rasu ne bayan tayi fama da gajeruwar rashin lafiya a gidan ta da ke Maiduguri a jihar Borno.

Majiyar ta ce, "Eh, tabbas ina tabbatar muku da cewa ta rasu.

"Ta rasu da yammacin yau kuma za a yi mata janaiza gobe da karfe takwas na safe.

"Allah ya jikan ta da rahama. Amin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164