COVID-19: An kwantar da Sarkin Daura a asibiti, yana ICU

COVID-19: An kwantar da Sarkin Daura a asibiti, yana ICU

- An kwanatar da Sarkin Daura, Alhaji Umar Faroouk Umar a asibitin tarayya da ke jihar Katsina

- Kamar yadda wata majiya daga fadar ta bayyana, basaraken na sashen kula na musamman a asibitin

- Ana zargin yana dauke da cutar korona bayan ya yi mu'amala da likitansa wanda aka tabbatar cutar ce ta kashe

An kwantar da Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar a sashen kula ta musamman ta asibitin tarayya da ke jihar Katsina.

Daura ce garin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wata majiya daga fada a ranar Talata ta ce an gaggauta mika Umar asibiti a daren Litinin kuma an kwantar da shi sakamakon mawuyacin halin da yake ciki.

Ana zargin Umar ya kwashi cutar COVID-19 daga likitan jihar Katsina, Dr Aminu Yakubu, wanda ya rasu sakamakon cutar a watan da ya gabata.

SaharaReporters ta gano cewa marigayi Yakubu ne likitan mai martaba sarkin Daura Umar Farouk da matarshi, Hajiya Binta Umar kafin mutuwarsa.

COVID-19: An kwantar da Sarkin Daura a asibiti, yana ICU

COVID-19: An kwantar da Sarkin Daura a asibiti, yana ICU. Hoto daga The Punch
Source: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Rashin abinci da magani yasa masu korona sun fito zanga-zanga a Gombe (Hotuna)

Matar sarkin Daura, Hajiya Binta Umar Farouk ta rasu a makonni biyu da suka gabata.

"A daren jiya ne aka hanzarta miki sarkin Daura asibitin tarayya da ke Katsina. A halin yanzu, an umarcemu da mu killace kanmu.

"Likitan da cutar ta kashe a jihar ya yi mu'amala da sarkin Daura da matarsa wacce ta rasu. Likitan ne ke duba lafiyar basaraken da matarsa.

"An umarci sarkin da ya killace kansa tun bayan mutuwar likitan amma bai saurara hakan ba. Ya bari ana shige da fice a fadar," majiyar ta sanar da SaharaReporters.

A ranar Litinin ne Dr Mustapha Inuwa, sakataren gwamnatin jihar Katsina yace an samu wasu masu dauke da cutar a fadar.

An diba samfur din mutum 89 amma har yanzu suna hannun NCDC don gwaji.

A wani labari na daban, wasu masu dauke da cutar korona da ke jinya a cibiyar killacewa ta Kwadon da ke karamar hukumar Yamaltu Dena ta jihar Gombe sun fito zanga-zanga.

A ranar Talata ne majinyatan suka fito zanga-zangar tare da rufe babbar hanyar Gombe zuwa Biu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel