Kaico! Yarinya yar shekara 6 ta kamu da cutar Coronavirus a jahar Jigawa
Wata karamar yarinya yar shekara 6 ta kamu da cutar Coronavirus mai toshe numfashi a garin karamar hukumar Kazaure na jahar Jigawa.
Gidan talabijin na Channels ta ruwaito kwamishinan kiwon lafiya na jahar, kuma shugaban kwamitin yaki da yaduwar Coronavirus a jahar, Abba Zakarine ya bayyana haka a ranar Talata.
KU KARANTA: Sai bayan bakka ake: Kalli yadda yaron Umar Musa Yar’adua ya tuna da mahaifinsa bayan shekara 10
Sai Zakarai yace dama mahaifin yarinyar shi aka fara samu da cutar a Kazaure bayan ya dawo daga wata tafiya da yayi zuwa jahar Enugu.

Asali: Twitter
Kwamishinan yace daga cikin mutane 18 da suka yi mu’amala da mahaifin yarinyar, kuma aka musu gwajin cutar Coronavirus, yarinyar ce kadai sakamakon gwajin ya nuna ta kamu da cutar.
Don haka Zakari ya ce zasu dauke yarinyar daga gidansu zuwa inda ake killace masu cutar a garin Dutse, babban birnin jahar Jigawa domin ta hadu da mahaifinta.
Sahihan alkalumma daga hukumar yaki da yaduwar cututtuka a Najeriya, NCDC, sun bayyana akwai mutane 39 dake dauke da cutar Coronavirus a Jigawa, yayin da mutum daya ya mutu.
A wani labari kuma, kwalejin horas da hafsoshin Sojin Najeriya, NDA ta kai gudunmuwar sinadarin wanke hannu ga gwamnatocin jahohin Kano da Jigawa don yaki da COVID19.
Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito kakaakin kwalejin, Manjo Abubakar Abdullahi ne ya bayyana haka a ranar Talata, 5 ga watan Mayu a garin Kaduna.
Abdullahi ya ce kwalejin ta dauki wannan mataki ne don bayar da gudunmuwarta ga rage yaduwar cutar Coronavirus a Najeriya tare da kawo karshensa a kasar.
Abubakar ya ce Birgediya Janar Ayoola Aboaba ne ya mika kayan a garin Kano da Dutse, inda yace manufar gudunmuwar shi ne domin taimaka ma kokarin da gwamnatocin suke yi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng