Dattijo mai shekara 100 da azumi a bakinsa ya yi tafiyar 40km don ya tara kudin taimakon mabukata

Dattijo mai shekara 100 da azumi a bakinsa ya yi tafiyar 40km don ya tara kudin taimakon mabukata

Cika shekaru 100 a duniya cikin koshin lafiya kan shi ba karamin niima bane ga dan adam sai dai baya da haka wani mazaunin binrin Landan, Dabir Choudhury yana kokarin yin wani abin mamaki da saoinsa ba za su iya aikatawa ba.

Dattijon ya yi tattaki na tsawon kilomita 40 a unguwarsu domin ya samu kudin da zai bai wa kungiyoyin tallafawa mutane 26 ciki har da wadanda za su tallafawa mutanen Gaza, Syria da Yemen.

Da farko Dabir ya yi alkawarin zai tara wa wadanda suka kamu da COVID-19 Dallar Amurka 1,250 a ranar Lahadi da ta gabata.

Ramadan: Dattijo mai shekara 100 ya yi tafiyar kilomita 40 don taimakawa 'yan gudun hijira
Ramadan: Dattijo mai shekara 100 ya yi tafiyar kilomita 40 don taimakawa 'yan gudun hijira. Hoto daga Just Giving
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Fargaba a Jigawa yayin da mutum 100 suka mutu cikin kwana 10

Ya yi alkawarin yin tattaki na tsawon kilomita 40 a unguwarsu kuma ya kammala duk da cewa yana azumi na watan Ramadan kamar yadda Middle East Monitor ta ruwaito.

Cikin awanni 9 da bude shafin karbar tallafi na Just Giving, mutane sun bayar da tallafin kudin da ake nema, bayan kwanaki biyu wasu mutane har da na kasashen waje suka fara aiko da nasu tallafin.

A halin yanzu dai jimillar kudin da aka tara wa Dabir domin tallafa wa mutane ya dara $7,515.

Ganin irin wannan goyon baya da tallafin da mutane ke bayar wa, Dabir ya sake yin alkawarin cewa ba zai dena yin tattakin ba muddin mutane za su cigaba da bayar da tallafin kudi.

Za a yi amfani da kudin da Dabir ya tara domin tallafawa kungiyoyin taimakon mutane 26 a kasashe daban daban don tallafawa masu fama da korona da kuma taimakawa mutane Gabas ta Tsakiya.

A sanarwar da ya fitar na godiya ga masu bayar da sadakan kudin, Dabir ya ce: Ina mika godiya ta saboda tallafin da kuke bayarwa. Ba ni kadai ke gwagwarmaya domin farantawa yara da ke rayuwa cikin yunwa ba rai ba, tare muke yi.

"Za ayi amfani da wannan kudin domin taimakawa iyalai masu bukata a Birtaniya, Bangladesh da sauran kasashen duniya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel