COVID-19: Yadda yunwa da mace-mace suka samu wurin zama a sansanin 'yan gudun hijira
- Mazauna sansanin gudun hijira na Durumi da ke Abuja sun koka da halin da suke ciki
- Sun tabbatar da cewa tsananin yunwa da rashin kula ta samu wurin zama a sansanin
- Dalilin haka ne yasa suke fita wurin neman abin saka wa a bakin salati duk da doka
"A sansanin aka barni tun safe. Muna shiga daji inda muke samo gyadar Kashu don ci saboda babu abinci. Kullum muke zuwa," cewar Mary.
Wadannan kalaman Mary Nuhu ce mai shekaru 14 wacce ke zama a sansanin 'yan gudun hijira da ke Durumi a yanki na daya da ke babban birnin tarayya Abuja. Sansanin 'yan gudun hijirar na nan a cikin birnin Abujan inda yake da a kalla mutum 2,830.

Asali: Twitter
Nuhu da sauran mazauna sansanin wadanda suka tsere daga kananan hukumomin Bama da Gwoza na jihar Borno suna cikin wani hali.
Sun samu mafaka a Abuja sannan gwamnatin tarayya ta amince su zauna a nan.

Asali: Twitter
A ranar Asabar da ta gabata, manema labarai sun kai ziyara sansanin inda suka tarar da Nuhu tare da sauran yaran sun shiga daji neman abinci.
A farfajiyar 'yan gudun hijira, akwai dakin shan magani, ma'adanar kayayyaki da kuma dakuna a kalla talatin a sansanini.
Wasu mata da maza tare da kananan yara ma zaune a kuniyance inda suke hira tare da gyara dorawa wacce suke cire kwayoyin daddawa.
"Wasu daga cikinmu suna zuwa cikin daji neman dorawa. Muna shan dorawar yayin da muke siyar da daddawar.
"Yaranmu na cike da yunwa a koda yaushe kuma suna kokawa a kan hakan," shugaban sansanin, Ibrahim Ahmed ya sanar da OrderPaperNG.

Asali: Twitter
Don samun ciyar da kananan yaran a yayin barkewar annobar nan, babu wata mafita da ta wuce su dinga neman mafita da kansu ta hanyar yin kananan ayyuka.
Hakan kuwa ne yasa ake take dokar hana walwalar da gwamnati ta gindaya na hana yaduwar cutar korona.
Jami'in hulda da jama'a na sansanin, wanda ya ce sunansa Umar Ali, ya ce mata da kananan yara ne abun tausayi a sansanin.
A duk lokacin da aka tashi raba wata gudumawa da aka samu daga jama'ar Annabi, su kan basu fifiko.
Shugaban sansanin ya bayyana yadda mutum biyu suka rasa rayukansu a sansanin sakamakon tsananin ciwon da ya kayar dasu da yunwa, jaridar The Cable ta ruwaito.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng