Boko Haram: Dakarun Nijar sun yi wa 'yan ta'adda ruwan wuta

Boko Haram: Dakarun Nijar sun yi wa 'yan ta'adda ruwan wuta

A ranar Lahadin da ta gabata ne rundunar sojin kasar Nijar suka fatattaki mayakan ta'addancin Boko Haram da suka kai musu hari a garin Diffa, babban birnin da ke yankin Kudu maso yamma na kasar.

Sanannen abu ne cewa an saba kai hari yankin Diffa da ke kusa da iyakar Najeriya tun a 2009, wata majiya daga cikin mazauna yankin ta tabbatar.

"Mun ji harbin bindiga da manyan makamai wurin karfe 4:30 na yamma zuwa 7 a yankin kudancin garin," Lawan Boukar, wani mazaunin yankin ya sanar a ranar Talata.

"Ashe mayakan Boko Haram ne suka kai hari na ba-zata. Tuni sojojin suka fatattake su har zuwa bayan gadar Douctchi," yace a yayin da yake nuni da gadar da ke tsallaken iyaka.

Wani mazaunin yankin ya ce, "Sun iso ne daga Najeriya da yammaci a yayin da ake shirin yin buda baki. Sun yi yunkurin daukar dakarunmu a ba-zata."

Wata majiya daga jami'an tsaro ta tabbatar da aukuwar lamarin amma bata bada bayanin yadda lamarin ya auku ba.

Boko Haram: Dakarun Nijar sun yi wa 'yan ta'adda ruwan wuta
Boko Haram: Dakarun Nijar sun yi wa 'yan ta'adda ruwan wuta. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Rashin abinci da magani yasa masu korona sun fito zanga-zanga a Gombe (Hotuna)

Hukumar tsaro da AFP ta tuntuba ta tabbatar da cewa za ta fitar da takardar bayanin yadda lamarin ya faru.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana, yankin tsakanin Najeriya da kasar Chadi ya saba samun harin mayakan ta'addancin tun a 2015.

Mayakan ta'addancin suna da maboya daban-daban a wurin tafkin Chadi inda iyakokin Kamaru, Chadi, Nijar da Najeriya suka hadu.

Harin ranar Lahadi ya biyo bayan ruwan wutar da mayakan suka ji ta sama da kasa daga dakarun Chadi inda suka halaka 'yan ta'adda masu yawa.

Kasar Chadi ta yi ikirarin cewa ta halaka dubban 'yan ta'addan amma ta rasa dakaru 52 a wannan musayar wutar.

A karshen watan Maris ne ma'aikatar tsaron Nijar ta yi ikirarin zama ta gaba wajen jagora a yaki da Boko Haram.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel