Gwamnatin Najeriya ta yaba wa kokarin Ganduje kan dakile yaduwar COVID-19 a Kano

Gwamnatin Najeriya ta yaba wa kokarin Ganduje kan dakile yaduwar COVID-19 a Kano

Gwamnatin tarrayar Najeriya ta yabawa gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje game da kokarin da ya ke yi domin dakile yaduwar annobar COVID-19 a jiharsa kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Idan ba a manta ba, Shugaba Buhari ya aike da kwamitin kar ta kwana na COVID-19 , PTF, karkashin jagorancin Dr Nasiru Gwarzo don tallafawa jihar wurin yaki da annobar.

A sanarwar da ta fitar a ranar Talata, Hadiza Namadi, Jamiar hulda da Jama'a a Ma'aikatar Lafiya ta Kano, ta ce Mr Gwarzo ya yi wannan yabon ne yayin zantawa da aka yi da tawagar yaki da annobar ta Kano.

An jiyo Mr Gwarzo yana yaba wa kokarin gwamnatin jihar tare da bayar da tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta cigaba da tallafawa jihar wurin yaki da annobar.

Gwamnatin Najeriya ta yaba wa kokarin Ganduje kan dakile yaduwar COVID-19 a Kano

Gwamnatin Najeriya ta yaba wa kokarin Ganduje kan dakile yaduwar COVID-19 a Kano. Hoto daga Daily Nigerian
Source: UGC

DUBA WANNAN: Fargaba a Jigawa yayin da mutum 100 suka mutu cikin kwana 10 Read more:

Sanarwar ta kuma ce an jiyo Dr Tijjani Hussain, jagoran tawagar yaki da annobar na jihar, yana cewa gwamnatin jihar ta dauki matakai na kare yaduwar cutar tun kafin bullar ta a jihar.

Mr Hussain ya ce, "Jihar ta samar da cibiyar killacewa da kayayykin da ake bukata domin dakile yaduwar annobar."

A cewar sanarwar, wakilan kwamitoci shida da ke aiki tare da kwamitin kar ta kwana na jihar sun yi wa PTF jawabi a kan ayyukansu da kallubalen da suke fuskanta wurin dakile yaduwar annobar.

Kallubalen da suka lissafa sun hada da; zirga-zirga, dakunan gwaji, sadarwa da kayan kulawa da marasa lafiya da sauransu.

A bangarensa, Hashim Imamudeen, shugban riko na kwamitin, ya ce gwamnatin jihar ta samar da kayayyakin kare kamuwa da cuta, PPE, takunkumin fuska, magunguna da abinci.

Ya yi bayanin cewa an rabar da PPE ga cibiyoyin killace mutane goma domin kare lafiyar ma'aikatan lafiya da ke kula da majinyata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel