An killace iyalan marigayi sarkin Kaura Namoda, an yi wa fadar feshi

An killace iyalan marigayi sarkin Kaura Namoda, an yi wa fadar feshi

Gwamnatin jihar Zamfara ta killace iyalan marigayi sarkin Kaura Namoda, Alhaji Ahmad Muhammad Asha.

Fadar sarkin tare da wasu manyan sassa na jihar duk an yi musu feshi kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.

Alhaji Asha ya rasu ne a ranar Lahadi bayan ya yi fama da da cutar ciwon sukari da hawan jini, kamar yadda kaninsa, Alhaji Abdulkarim Ahmad Asha ya sanar.

Amma kuma, akwai hasashen da ke bayyana cewa akwai yuwuwar basaraken ya samu cutar korona kafin rasuwarsa.

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, wanda ya yi jawabi a kan wannan ci gaban, ya ce gwamnatin na kokarin shawo kan annobar.

An killace iyalan marigayi sarkin Kaura Namoda, an yi wa fadar feshi

An killace iyalan marigayi sarkin Kaura Namoda, an yi wa fadar feshi
Source: UGC

Ya sanar da rufe kasuwanni jihar tare da dakatar da sallolin jam'i a masallatai da majami'un fadin jihar.

Mai bada shawara na musamman ga gwamnan a fannin yada labarai, Zailani Bappa, ya ce gwamnan ya sake jaddada dokar ta baci a jihar data karfe 8 na yamma zuwa 6 na safe.

A karamar hukumar Kaura Namoda kuwa, daga karfe 6 na yamma ne zuwa 6 na safe.

Ya ce wannan sabon matakin na tsawon mako daya ne.

Amma kuma gwamnan ya jajanta halayyar rashin kula da jama'ar jihar me nuna wa ta yadda suke take dokokin kiyaye yaduwar cutar.

Ya ce rufe kasuwannin bai shafi shagunan magunguna ba da manyan shaguna, amma gwamnati za ta tabbatar da cewa an bi dokokin yadda ya dace.

KU KARANTA KUMA: Duk mun ji kunya – Dino Melaye ya caccaki yan siyasa, ya ce dukkaninsu sun gaza

Gwamnan ya yi kira ga jama'ar jihar da su yi sallolinsu a gida saboda hakan bai take dokokin addinin Musulunci ba don shawo kan annoba.

Ya ce sabbin dokokin za a kara duba su nan gaba kadan don sanin matakin dauka na gaba.

A baya mun ji cewa Sarkin Kiyawan Kauran Namoda a jihar Zamfara, Alhaji Muhammad Ahmad Asha ya rasu.

Ya rasu yana da shekaru 71 a duniya, ya kuma bar mata uku da yaya da dama.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel