Da duminsa: Rashin abinci da magani yasa masu korona sun fito zanga-zanga a Gombe (Hotuna)

Da duminsa: Rashin abinci da magani yasa masu korona sun fito zanga-zanga a Gombe (Hotuna)

- A yau Talata ne wasu masu jinyar cutar Korona a jihar Gombe suka fito zanga-zanga sakamakon zargin gwamnati da suka yi da rashin kula

- Kamar yadda suka bayyana, gwamnati ta killacesu ne a cibiyar killacewa ta Kwadon da ke karamar hukumar Yamaltu Dena ta jihar Gombe

- Kamar yadda hotunan suka bayyana, masu fama da cutar sun rufe babban titin Gombe zuwa Biu inda suke korafin rashin abinci da magani

Wasu masu dauke da cutar korona da ke jinya a cibiyar killacewa ta Kwadon da ke karamar hukumar Yamaltu Dena ta jihar Gombe sun fito zanga-zanga.

A ranar Talata ne majinyatan suka fito zanga-zangar tare da rufe babbar hanyar Gombe zuwa Biu.

An gano cewa majinyatan na zanga-zangar ne sakamakon halin-ko-in-kula da gwamnatin jihar ta nuna musu. Sun rasa abinci da magunguna duk da kuwa killacesu da aka yi.

Da duminsa: Rashin abinci da magani yasa masu korona sun fito zanga-zanga a Gombe (Hotuna)
Da duminsa: Rashin abinci da magani yasa masu korona sun fito zanga-zanga a Gombe (Hotuna). Hoto daga SaharaReporters
Asali: Twitter

Wani mazaunin yankin wanda ya samu zantawa da jaridar SaharaReporters, ya ce, "Tabbas sun baro cibiyar killacewar kuma a halin yanzu suna tarwatsa dukiyoyin jama'a a kan babban titin.

"Abin takaici ne yadda majinyatan suka fito zanga-zanga. Gaskiya gwamnati bata yi musu adalci ba."

KU KARANTA: Yadda wata mata ta dinga falla wa dan sanda mari (Bidiyo)

Kamar yadda hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta NCDC ta tabbatar, jihar Gombe na da mutum 96 da aka tabbatar suna dauke da kwayar cutar.

Da duminsa: Rashin abinci da magani yasa masu korona sun fito zanga-zanga a Gombe (Hotuna)
Da duminsa: Rashin abinci da magani yasa masu korona sun fito zanga-zanga a Gombe (Hotuna). Hoto daga SaharaReporters
Asali: Twitter

A yayin da aka tuntubi kwamishinan lafiya na jihar Gombe, Ahmed Gana ya ki daga kiransa.

Hakazalika, jami'an ma'aikatar lafiya ta jihar sun tabbatar wa da jaridar SaharaReporters aukuwar lamarin.

A wani labari na daban, a wani bidiyo da ya yawaita a kafar sada zumuntar zamani, an ga wata mata na marin dan sanda a jihar Oyo.

Matar mai yara shida mai suna Kehinde Afolake, ta shiga hannun jami'an 'yan sanda sakamakon cin zarafin da tayi wa dan sanda mai mukamin ASP kuma DCO din ofishin 'yan sanda na Eruwa mai suna Adeyemi Ogunyemi.

Adeyemi, wanda ya nuna jarumta, ya tsaya a bidiyon inda matar ta dinga falla mishi mari har sau 13.

Ya jagoranci rundunar 'yan sanda ne don tabbatar da dokar hana walwala a Gbolagunte da ke yankin Okeola a Ibarapa ta jihar Oyo a ranar 1 ga watan Mayu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel