Yanzu-yanzu: SGF, ministan lafiya da shugaban NCDC sun gurfana gaban majalisar tarayya

Yanzu-yanzu: SGF, ministan lafiya da shugaban NCDC sun gurfana gaban majalisar tarayya

- Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin yaki da cutar korona na kasa, Boss Mustapha, tare da ministan lafiya sun bayyana a gaban majalisar tarayya

- Sun samu rakiyar shugaban hukumar NCDC, Dr Chikwe Ihekweazu don bayanin matakin da suka dauka da kuma hanyar shawo kan matsalar

- A makon da ya gabata ne majalisar wakilan kasar nan ta yanke shawarar kiran shugabannin uku bayan tafka mahawara a zauren majalisar

Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya da ministan lafiya, Osagie Ehanire, sun bayyana a gaban majalisar wakilan Najeriya a yau don bayani a kan mace-macen jihar Kano.

Su biyun sun samu rakiyar Dr Chikwe Ihekweazu, darakta janar din hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) a yau Talata.

Yanzu-yanzu: SGF, ministan lafiya da shugaban NCDC sun gurfana gaban majalisar tarayya
Yanzu-yanzu: SGF, ministan lafiya da shugaban NCDC sun gurfana gaban majalisar tarayya. Hoto daga jaridar The Cable
Asali: Twitter

Sun je bayani ne ga majalisar a kan kokarin da suke yi don shawo kan annobar COVID-19 a kasar nan, kamar yadda jaridar The Cable ta wallafa.

Tun bayan da aka fara samun mai cutar a ranar 11 ga watan Afirilun 2020 a jihar Kano, jihar ta ci gaba da fuskantar mace-mace masu matukar bada mamaki wanda ake alakantawa da kwayar cutar.

Daga bisani, kwamitin fadar shugaban kasa a kan yaki da cutar COVID-19 ta tabbatar da cewa cutar na da babbar alaka mace-macen.

Yanzu-yanzu: SGF, ministan lafiya da shugaban NCDC sun gurfana gaban majalisar tarayya
Yanzu-yanzu: SGF, ministan lafiya da shugaban NCDC sun gurfana gaban majalisar tarayya. Hoto daga jaridar The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda wata mata ta dinga falla wa dan sanda mari (Bidiyo)

Bayan tafka mahawara a kan mace-macen a makon da ya gabata, 'yan majalisar sun yanke hukuncin kiran shugabannin uku don bada amsa a kan kalubalen tare da samo hanyar shawo kan barkewar cutar a Najeriya.

Sun kara da yanke hukuncin cewa za su tuntubi sarakunan gargajiya da na addinai don kokarin kawo karshen matsalar.

Yanzu-yanzu: SGF, ministan lafiya da shugaban NCDC sun gurfana gaban majalisar tarayya
Yanzu-yanzu: SGF, ministan lafiya da shugaban NCDC sun gurfana gaban majalisar tarayya. Hoto daga jaridar The Cable
Asali: Twitter

A halin yanzu, jihar Kano na da majinyata 365 daga cikin 2,802 da ke fama da cutar a Najeriya, kamar yadda NCDC ta bayyana.

Mutum 93 ne suka rasu sakamakon annobar Coronavirus a Najeriya. Hukumar kula da cutuka masu yaduwa ta NCDC ce ta sanar da hakan a shafinta na Twitter a ranar Litinin.

A daren Litinin ne hukumar ta sanar da kara samun sabbin masu cutar har 245 duk da an sallama mutum 417 daga asibiti sakamakon jinya daga cutar.

Duk da dai, gwamnatin tarayya ta dauka alwashin sake rufe wasu sassan kasar nan matukar yawan masu cutar ya ci gaba da karuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel