COVID-19: Mai maganin gargajiya zai yi wa majinyata magani kyauta

COVID-19: Mai maganin gargajiya zai yi wa majinyata magani kyauta

Wani mai maganin gargajiya a jihar Ondo, Dr Ola Olasumbo, ya bukaci gwamnatin tarayya ta bashi damar yiwa wasu masu fama da COVID-19 magani kyauta.

Gwamna Oluwarotimi Akeredolu a makon da ta gabata ya ce jihar za ta fara amfani da magungunan gargajiya domin yi wa masu korona magani.

Akeredolu ya ce zai gwada amfani da magungunan da sarakuna kamar Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi suka ambata.

Sarakunan sun shawarci gwamnati ta fara gwada magungunan gargajiya.

COVID-19: Mai maganin gargajiya zai yi wa majinyata magani kyauta

COVID-19: Mai maganin gargajiya zai yi wa majinyata magani kyauta. Hoto daga Guardinan Ng
Source: UGC

DUBA WANNAN: Ganduje ya sassauta dokar kulle a Kano, ya sanar da ranakun walwala

Olasumbo ya ce ya amsa kirar ta Gwamna Akeredolu a kan amfani da magungunan gargajiya wurin magancen COVID-19 da duk alamomin da cutar ke haifar wa.

Mai maganin gargajiyar, da ya yi magana da yan jarida a Akure, babban birnin jihar ya ce, "A lokacin da aka samu bullar cutar a China da wasu kasashen duniya, kungiyar masu maganin gargajiya ta Najeriya sun yi taro sun kuma amince kowa ya koma ya fara bincike don gano maganin ta.

"Bayan watanni ina bincike, na gano maganin cutar. Amma ina jirar amincewar Hukumar NAFDAC domin fara yin gwaji a kan majinyata.

"A baya, na kirkiri magunguna wadanda ke magance cutar kyanda da karambau da wasu cututtukan da ke kisa. Saboda haka, ina fatan da wannan maganin, an ci galaba a kan COVID-19."

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya ce jihar ta samu karin mutum daya da ke dauke da cutar Korona. Hakan ya kai masu dauke da cutar a jihar zuwa 12.

Sule ya bayyana hakan ne a yayin jawabi ga taron jami'an tsaro a ranar Talata a garin Lafia.

Gwamnan ya ce, wanda ya sake kamuwar direban hukumar kula da cutuka masu yaduwa ne, NCDC, wanda ke dibar samfur daga jihar zuwa hukumar da ke Abuja.

Ya ce direban na zama a karamar hukumar Karu ne da ke jihar kuma an gano yana dauke da cutar a ranar Talata.

Kamar yadda jaridar The Nation ta bayyana, Gwamnan ya ce an mika mara lafiyar zuwa cibiyar killacewa da ke asibitin tarayya da ke Keffi domin bashi kulawar kwararru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel