Fargaba a Jigawa yayin da mutum 100 suka mutu cikin kwana 10

Fargaba a Jigawa yayin da mutum 100 suka mutu cikin kwana 10

Mutane a Jigawa sun shiga fargaba a yayin da aka ruwaito cewa fiye da mutane 100 sun mutu cikin kwanaki 10 da suka shude a karamar hukumar Hadejia na jihar kamar yadda Daily trust ta ruwaito.

Rahoton ya saka gwamnatin ta kafa kwamiti mai mutane biyar domin gudanar da bincike a kan dalilin mace-macen kamar yadda hukumomi suka bayar da shawara.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dr Abba Zakari, wanda kuma shine shugaban kwamitin kar ta kwana na COVID 19 a jihar ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

A cewarsa, Dr Mahmud Abdulwahab ne zai jagoranci kwamitin tare da Shehu Mohammad, Yusuf Hakimi, Shehu Sule da wakilan Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, a matsayin mambobi.

Fargaba a Jigawa yayin da mutum 100 suka mutu cikin kwana 10
Fargaba a Jigawa yayin da mutum 100 suka mutu cikin kwana 10. Hoto daga Channels TV
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Ganduje ya sassauta dokar kulle a Kano, ya sanar da ranakun walwala

Abba Zakari ya bayyana cewa ana sa ran kwamitin za ta fitar da rahoton ta cikin kwanaki uku.

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan Kwamitin Shugaban Kasa da aka aike zuwa jihar Kano domin tallafawa kwamitin jihar domin gano dalilan mace mace a jihar ta fitar da rahoton ta inda ta ce COVID-19 ne ke kashe mutane.

Shugaban tawagar, Dr Nasiru Sani Gwarzo ne ya bayyana hakan yayin hira da ya yi da yan jarida a Kano yayin da ya ke gabatar da rahoton kwamitin tare da mika dakin gwajin da Gidauniyar Dangote ta bai wa gwamnatin Kano.

Ya yi bayanin cewa cutar coronavirus ce ta yi sanadin yawaitan mace macen da aka samu a Kano a baya bayan nan.

Dr Gwarzo ya ce bayan tattara bayanai da tambayoyi da aka yi wa iyalan wadanda suka mutu, an gano cewa COVID-19 ne ya yi sanadin mafi yawancin mace mace a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel