Shugaban kasar Togo Gnassingbe ya amshi rantsuwar mulki karo na 4
Shugaban kasar Togo, Faure Gnassingbe ya amshi rantsuwar mulki karo na hudu a ranar Lahadi, a wani kwarya kwaryan taro da aka shirya don kare yaduwar Coronavirus.
Punch ta ruwaito mutane 200 kacal aka gayyata zuwa wajen taron, kuma dukkansu suna sanye da takunkumi tare da sanya tazara a tsakaninsu har aka kammala bikin amsan rantsuwar.
KU KARANTA: Badakalar kudin Abacha: Najeriya ta samu zambar kudi dala miliyan 311 daga kasashen waje
Da yake kasar ta garkame iyakokinta a dalilin kare yaduwar cutar Coronavirus, hakan tasa jakadun kasashen waje ne kadai suka wakilce shuwagabannin kasashen su a taron.
Gnassingbe mai shekaru 53 ya samu nasara a zaben shugaban kasa daya gudana a kasar Togo ne bayan ya lashe zaben da ruwan kuri’u fiye da abokan hamayyarsa.
A yanzu dai shugaba Gnassingbe zai zarce wa’adin mulki na hudu ne bayan kwashe shekaru 15 a kan karagar mulki, kowanne wa’adin mulki a kasar Togo shekara biyar ne.
Sai dai bayan kammala zaben, babban abokin hamayyar Gnassingbe, tsohon firai ministan kasar, Agbeyome Kodjo wanda ya samu kashi 18.37 na kuri’un da aka kada ya zaben ya yi bore.
Kodji ya nuna rashin amincewarsa da nasarar shugaba Gnassingbe, har ta kai gay a sanar da kansa a matsayin zababben shugaban kasar a watan Afrilu.
Wannan bore tare da wuce gona da iri da yayi tasa gwamnatin kasar Togo ta umarci rundunar Sojojin kasar su kama shi, inda har yanzu yana daure tun watan Afrilu.
A hannu guda, kasar Togo na fama da yaduwar Coronavirus, wanda a yanzu ta kama mutane 123, ta kashe mutane 9 , kamar yadda hukumar kare yaduwar cututtuka ta kasar ta bayyana.
A wani labarin kuma, gwamnatin Amurka da ta Bailiwick of Jersey sun aiko ma Najeriya dala miliyan 311 daga cikin kudaden da tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha ya taskance a can.
Ministan sharia, Abubakar Malami ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin ta bakin hadiminsa a kan harkar watsa labaru, Dakta Umar Gwandu.
Malami ya bayyana cewa kasashen biyu sun aiko ma Najeriya $311,797,866.11, wanda ya haura kudin da suka yi alkawarin aikowa tun a watan Feburairun 2020, watau $308m.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng