Gwamnan Katsina ya bayyana abin da yasa gwamnati ta garkame fadar masarautar Daura

Gwamnan Katsina ya bayyana abin da yasa gwamnati ta garkame fadar masarautar Daura

Gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana dalilin da yasa gwamnati ta dauki matakin garkame fadar masarautar Daura a karshen makon da ta gabata.

Daily Trust ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin da ganawa da manema labaru, inda yace suna fargabar samun bullar Coronavirus a fadar ne.

KU KARANTA: Badakalar kudin Abacha: Najeriya ta samu zambar kudi dala miliyan 311 daga kasashen waje

“Fadar masarauta, kamar gidan gwamnati ne, wuri ne dake cike da mutane da dama, don haka muka yanke shawarar kula da lamarin ta hanyar yi ma mazauna fadar gwaji, a haka mun yi ma mutane 89 gwaji.

“A yanzu dai muna jiran samun sakamakon gwajin nasu, daga nan zamu san mataki na gaba da zamu dauka, shi yasa kaga muka mamaye fadar kamar yadda Sojoji suke yin juyin mulki, ta haka ne kadai zamu iya gane wadanda ke dauke da cutar a fadar.” Inji shi.

Gwamnan Katsina ya bayyana abin da yasa gwamnati ta garkame fadar masarautar Daura
Fadar masarautar Daura Hoto:TheCable
Asali: UGC

Gwamnan ya kara da cewa jahar Katsina na fuskantar manyan kalubale guda biyu, annobar Covid-19 da kuma hare haren yan bindiga dake cigaba da cin karensu babu babbaka har yanzu.

Amma ya bada tabbacin kokarin da gwamnati ke yi na shawo kan matsalolin, inda a yanzu haka Sojoji sun kaddamar da samame a dajin Jibia don kashe yan bindigan.

Sa’annan gwamnonin Arewa 19 na kokarin sayo kayayyakin gwaje gwajen Covid-19 daga kasar Afirka ta kudu domin samar da isassun kayan aikin da ake bukata a cibiyoyin gwajin cutar.

A wani labari kuma, Ma’aikatan kiwon lafiya guda 14 sun kamu da annobar cutar Coronavirus a jahar Katsina, kamar yadda gwamnan jahar, Aminu Bello Masari ya tabbatar.

Masari ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 4 ga watan Mayu, inda yace ma’aikatan na daga cikin sabbin mutane 37 da suka kamu da cutar daga ranar 2 zuwa 4 ga watan Mayu a jahar.

Wanda ya fara mutuwa daga cutar shi ne Dakta Aliyu Yakubu, babban likita a garin Daura, kuma shi ya fara kamuwa da cutar bayan ya dawo daga tafiyar da ya yi zuwa jahar Legas.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel