Jami’an kiwon lafiya guda 14 sun kamu da Coronavirus a jahar Katsina

Jami’an kiwon lafiya guda 14 sun kamu da Coronavirus a jahar Katsina

Ma’aikatan kiwon lafiya guda 14 sun kamu da annobar cutar Coronavirus a jahar Katsina, kamar yadda gwamnan jahar, Aminu Bello Masari ya tabbatar.

Daily Trust ta ruwaito Masari ya bayyana haka ne a ranar Litinin, inda yace ma’aikatan na daga cikin sabbin mutane 37 da suka kamu da cutar daga ranar 2 zuwa 4 ga watan Mayu a jahar.

KU KARANTA: Badakalar kudin Abacha: Najeriya ta samu zambar kudi dala miliyan 311 daga kasashen waje

Gwamnan ya ce ba wai ma’aikatan suna kula da masu cutar bane, amma sun kamu ne ta hanyar kula da sauran marasa lafiya kamar yadda suka saba yi a asibitoci daban daban.

Jami’an kiwon lafiya guda 14 sun kamu da Coronavirus a jahar Katsina
Likitoci Hoto: Katsinapost
Asali: UGC

“Zuwa yanzu muna da mutane 75 da suka kamu da cutar a Katsina, mun sallami 6 daga cikinsu, daga cikin sabbin mutane 37 da suka kamu, 14 ma’aikatan asibiti ne duk da cewa ba wai suna kula da masu cutar bane.

“Jami’ai ne dake duba marasa lafiya daban daban da suka tafi asibiti da matsaloli daban daban, amma ashe suna dauke da cutar Coronavirus ba’a sani ba, daga cikin ma’aikatan, 10 suna aiki a cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya ne, 4 kuma a asibitoci masu zaman kansu.

“22 daga cikin wadanda suka rage suna nan a garin Katsina, yayin da guda 1 ke garin Daura.” Inji shi.

A ranar Lahadi ne aka samu karin mutane 8 dauke da cutar Coronavirus a Katsina, kamar yadda hukumar kare yaduwar cututtuka, NCDC ta sanar, yayin da mutane 7 suka mutu daga cutar.

Wanda ya fara mutuwa daga cutar shi ne Dakta Aliyu Yaukubu, babban likita a garin Daura, kuma shi ya fara kamuwa da cutar bayan ya dawo daga tafiyar da ya yi zuwa jahar Legas.

A wani labarin kuma, yayin da aka sassauta dokar hana fita a Legas, Ogun da babban birnin tarayya Abuja, likitoci sun gargadi yan Najeriya game da hadarin yin biris da dokokin kare kai.

Likitocin a karkashin kudin Association of Resident Doctors, ARD, sun bayyana cewa gwamnati za ta kara garkame mutane idan har aka samu yaduwar cutar Coronavirus a wannan lokaci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel