Yadda wata mata ta dinga falla wa dan sanda mari (Bidiyo)

Yadda wata mata ta dinga falla wa dan sanda mari (Bidiyo)

A wani bidiyo da ya yawaita a kafar sada zumuntar zamani, an ga wata mata na marin dan sanda a jihar Oyo.

Matar mai yara shida mai suna Kehinde Afolake, ta shiga hannun jami'an 'yan sanda sakamakon cin zarafin da tayi wa dan sanda mai mukamin ASP kuma DCO din ofishin 'yan sanda na Eruwa mai suna Adeyemi Ogunyemi.

Adeyemi, wanda ya nuna jarumta, ya tsaya a bidiyon inda matar ta dinga falla mishi mari har sau 13.

Ya jagoranci rundunar 'yan sanda ne don tabbatar da dokar hana walwala a Gbolagunte da ke yankin Okeola a Ibarapa ta jihar Oyo a ranar 1 ga watan Mayu.

A bidiyon, an ga yadda matar ta dinga falla wa Adeyemi mari tare da ihun cewa shi ke marinta.

A yayin da take bayani ga jama'a da suka taru, ta dinga waska wa dan sandan mari inda taron jama'ar ke kara mata kaimi ta hanyar ihu.

A maimakon ya rama, an ji yana tsawatarwa ga jama'ar da ke kokarin kwatarsa daga hannun matar.

An zargi matar da cizon 'yar sandar da ta je kamata har gida sakamakon marin dan sanda washegari. Daga bisani dai an wuce da ita ofishin 'yan sanda.

KU KARANTA: Mace-macen Kano: Yadda jarumin Kannywood ya yanke jiki ya fadi

A yayin tsokaci game da wannan bidiyon, sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya jinjinawa Adeyemi da ya bayyana juriya tare da kwarewar aikinsa.

"Matar ta ci zarafin wasu 'yan sanda biyu daban. Sifeta Ojola Abiola da Sifeta Queen Eguaoje duk sun koka sakamakon cizon da ta garza musu a ranar Asabar, 2 ga watan Mayun 2020 yayin da suka je kamata," cewar IGP din ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya.

Ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa ba za su lamunci ire-iren wannan cin zarafin ba.

Ya bayyana cewa, a yayin tabbatar da dokar hana walwalar, 'yan sanda 27 ne suka koka da cin zarafi tare da harin da aka dinga kai musu kashi daban-daban.

Kamar yadda IGP ya bayyana, wasu daga cikin jami'an na asibiti sakamakon raunikan da suka samu daga hare-haren.

A don haka ya umarci kwamishinan 'yan sanda na jihar Oyo da ya yi bincike a kan lamarin tare da tabbatar da cewa an yi adalci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel