Coronavirus: Masu bincike na jami'ar FUTA sun bayar da shawara a kan shan shayin zobo da citta domin bunkasa garkuwar jiki

Coronavirus: Masu bincike na jami'ar FUTA sun bayar da shawara a kan shan shayin zobo da citta domin bunkasa garkuwar jiki

A yayin da likafar annobar korona ke ci gaba babu sassauci, wata kungiyar masu bincike a Jami'ar Fasaha ta Akure da ke jihar Ondo, ta yi wani bincike kan muhimmancin shan zobo domin bunkasa garkuwar jiki.

Sanadiyar yadda kawo yanzu ba a samar da maganin cutar korona ba, a halin yanzu dai ingatacciyar garkuwar jiki ita kadai ce ke iya yakar cutar a jikin mutum kamar yadda mahukuntan lafiya suka bayyana.

Kwararrun masanan na jami'ar FUTA sun bayar da sharawa a kan muhimmancin bunkasa garkuwa jiki ta hanyar sarrafa shayin zobo da citta da kuma garin cocoa, sunadarin da ake hada cakulan da shi.

Jagoran masu binciken da ya kasance kwararren masani a fannin kimiya da fasahar abinci, Farfesa Nathaniel Fagbemi, ya ce wannan hadi yana da ikon bunkasa garkuwar jiki ta hanyar bayar da rigakafin cututtuka masu yaduwa a tsakanin mutane.

Garin shayin da masanan suka hada ya samo asali ne daga ganyen zobo, itacen citta da kuma garin cocoa.

Ganyen Zobo

Ganyen Zobo
Source: UGC

Bincikensu ya tabbatar da cewa, wannan garin shayin yana da tarin albarka ta sunadaran antioxidants, masu taka rawar gani wajen bai wa jiki kariya da kuma garkuwa ta yakar cututtuka.

Bisa dogaro da wannan bincike, hakika sun yi itifakin cewa wannan hadi na wadartar da jiki tare da bayar da rigakafin kamuwa da cututtuka da kuma kariya ta harbin kwayoyin cuta.

KARANTA KUMA: Maganin gargajiya na kasar Madagascar ba ya warkar da cutar korona - WHO

Masu binciken sun ce wannan hadi yana da muhimmanci ga rayuwa musamman a lokacin shakar iska da bude kafofin numfashi.

Shakar iska wadatacciya tana da alakar inganta lafiyar kwayoyin halittu wajen kashe kwayoyin cututtuka masu tayar da hankali kamar su cutar daji, cututtukan zuciya, ciwon sukari, raunin jiyoyi masu isar da sako zuwa kwakwalwa da raunata tsarin garkuwar jiki.

A yanzu dai jami'ar FUTA ta fidda wannan ganyen shayi na zobo, citta da kuma sunadarin hada cakulan a cikin leda kuma ya yi tallarsa tare da bajakoli a taron nuna bajintar kimiyya da dama da Hukumar jami'o'in Najeriya ta gudanar.

Jami'ar ta kuma ce ta kammala duk wani shirin na samun hadin gwiwar Hukumomin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da suka nuna ra'ayinsu a kai domin samar da ganyen shayin a babban masaki.

Shugaban jami'ar, Joseph Fuluwape, ya ce jami'ar za ta ci gaba da zage dantse wajen tunkarar halin da Najeriya da kuma Duniya ta ke ciki domin fuskantar kalubale ta hanyar bincike da kuma kawo ci gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel