Najeriya za ta farfado da karfinta bayan gushewar Coronavirus – Mataimakin shugaban kasa

Najeriya za ta farfado da karfinta bayan gushewar Coronavirus – Mataimakin shugaban kasa

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya jinjina ma juriyar yan Najeriya, inda yace Najeriya za ta farfado da karfinta bayan gushewar annobar Coronavirus.

Punch ta ruwaito Osinbajo ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar ta hannun hadiminsa akan watsa labaru, Laolu Akande a yayin da yake gabatar da jawabi a taron The Platform 2020.

KU KARANTA: Abubuwa 4 da ya kamata masoya su sani game da junansu kafin aure

A jawabinsa, Osinbajo ya ce: “Za mu farfado daga wannan ibtila’I da karfin mu saboda juriyarmu, da kuma karfin tattalin arziki, akwai kalubale da dama, amma kuma akwai dama sosai na sauya yadda abubuwa suke.”

Najeriya za ta farfado da karfinta bayan gushewar Coronavirus – Mataimakin shugaban kasa

Mataimakin shugaban kasa Osinbajo Hoto: Punch
Source: UGC

Osinbajo ya zayyana wasu matakai da gwamnati ke dauka na farfado da tattalin arzikin kasar da ya samu tangarda a dalilin Coronavirus, inda yace:

“Mun mayar da hankali wajen amfani da kayan gida wajen gine gine manyan ayyuka. Misali, a aikin ginin tituna, ya fi sauki a yi amfani da duwatsun siminti a kan kashe makudan kudade wajen shigo da kwalta.

"Muna da duwatsu siminti birjik a kasar nan, don haka nan za mu karkata, a yanzu haka hanyar Apapa zuwa titin Legas-Ibadan da siminti muke yin sa.

“A bangaren ginin gidaje kuwa, akwai gibi sosai a wajen, dole ne anan ma mu mayar da hankalinmu wajen amfani da kayan gida, daga haka sai mu samar da daman aiki ga injiniyoyinmu, masana masu zanen gine gine da magina dss.” Inji shi.

A bangaren noma kuwa, Osinbajo yace gwamnatin Buhari ta riga ta ceto kasar nan daga dogara da kasashen waje wajen samun abinci ta hanyar inganta hanyar noma a gida.

“Muna ganin idan muka cigaba da habbaka noma, musamman ga kananan manoma tare da samar da rumbunan ajiye abinci, za’a samu ayyuka da yawa ta bangaren matasa, da haka zamu kara rage shigo da abinci daga kasashen waje, mu inganta namu abincin da kuma samar da aikin yi.”

Sauran wadanda suka yi jawabi a taron wanda aka gudanar da shi ta yanar gizo sun hada da gwamnan jahar Ekiti, Kayode Fayemi, Nasir El-Rufai na Kaduna, Ifeanyi Okowa na Jahar Delta.

Sai gwamnan jahar Nassarawa, Abdullahi Sule, gwamnan jahar Edo Godwin Obaseki da kuma shugaban hukumar kula da yaduwar cututtuka, Dakta Chike Ihekweazu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel