Masu cutar Coronavirus 50 cikin 59 a Kaduna almajirai ne – El-Rufai

Masu cutar Coronavirus 50 cikin 59 a Kaduna almajirai ne – El-Rufai

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa daga cikin mutane 59 dake dauke da cutar Coronavirus a jahar Kaduna, 50 daga cikinsu almajirai ne.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, a shafinsa na kafar sadarwar zamani na Twitter, inda yace samun almajirai 50 masu cutar yasa jahar ke da muutane 59 dake da cutar.

KU KARANTA: Abubuwa 4 da ya kamata masoya su sani game da junansu kafin aure

A lissafin hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC, jahar Kaduna na da mutane 66 da suka kamu da cutar Coronavirus, daga cikinsu har da gwamnan jahar.

Sai dai zuwa yanzu jahar ta sallami gwamnan da wasu mutane biyar bayan sun warke daga cutar bayan daukan mabanbanta lokuta suna killace. Amma an samu mutum daya da ya mutu.

Yawancin almajiran da gwamnan ke magana a kan su yan asalin jahar Kaduna ne, amma suka tafi jahar Kano almajiranci, don haka gwamnatin jahar Kano ta mayar dasu jahar Kaduna.

Bayan an mayar da su Kaduna ne sai gwamnatin jahar ta amshe su, ta killace da nufin gudanar da gwajin cutar COVID19 a kansu kafin ta sake su, a haka ne aka gano suna dauke da cutar.

A hannu guda kuma hukumar NCDC ta sake sakin sabbin bayanai game da yaduwar cutar Coronavirus a Najeriya, inda a tace a yanzu an samu karin mutane 170 masu cutar a Najeriya.

NCDC ta bayyana haka ne a shafinta na Twitter inda tace akwai jimillan mutane 2558 dake dauke da cutar a Najeriya, 400 sun warke yayin da wasu 87 suka mutu.

Jerin jahohin da aka samu karin cutar sune: 39-Lagos 29-Kano 24-Ogun 18-Bauchi 15-Kaduna 12-FCT 12-Sokoto 8-Katsina 7-Borno 3-Nasarawa 2-Adamawa da kuma mutum 1 a jahar Oyo.

A wani labari kuma, yan bindiga sun kai farmaki wani kauyen Dande dake cikin karamar hukumar Chikun a jahar Kaduna, inda suka kashe yan banga guda hudu, suka jikkata 2.

Daily Trust ta ruwaito lamarin ya faru ne a ranar Juma’a yayin da yan bindigan suka yi ma yan bangan kwantan bauna a kauyen da bai wuce nisan kilomita 4 zuwa kauyen Buruku ba.

Yan bindigan suna kan hanyar su ta zuwa dauko gawar wani direban mota da wasu gungun miyagu yan bindiga suka kashe ne, a wannan lokaci ne yan bindigan suka far musu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel