Miyagu sun cigaba da cin karen su babu babbaka a Kaduna duk da dokar Corona

Miyagu sun cigaba da cin karen su babu babbaka a Kaduna duk da dokar Corona

Wasu gugun miyagun yan bindiga sun kai farmaki wani kauyen Dande dake cikin karamar hukumar Chikun a jahar Kaduna, inda suka kashe yan banga guda hudu, suka jikkata 2.

Daily Trust ta ruwaito lamarin ya faru ne a ranar Juma’a yayin da yan bindigan suka yi ma yan bangan kwantan bauna a kauyen da bai wuce nisan kilomita 4 zuwa kauyen Buruku ba.

KU KARANTA: Abubuwa 4 da ya kamata masoya su sani game da junansu kafin aure

Yan bindigan suna kan hanyar su ta zuwa dauko gawar wani direban mota da wasu gungun miyagu yan bindiga suka kashe ne, a wannan lokaci ne yan bindigan suka far musu.

Wani mazaunin yankin, Malam Umaru ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana harin a matsayin abin bakin ciki ga al’ummar Buruku saboda muhimmancin yan bangan.

Umaru ya cigaba da fadin yan bangan suna taka muhimmiyar rawa wajen kare al’ummar kauyukan dake yankin daga hare haren yan bindigan da suke yawan kai musu hari.

Miyagu sun cigaba da cin karen su babu babbaka a Kaduna duk da dokar Corona

Dan bindiga Hoto: Vanguard
Source: Facebook

“Muna cikin jimami, muna alhinin mutuwar yan bangan nan guda hudu da yan bindiga suka kashe mana a ranar Juma’a sunayensu Habibu Yusuf, Adam Abubakar, Buhari Kabiru ‎da Sani Abdullahi.

“Wadanda suka samu rauni kuma sun hada da Abdulrazak Abdullahi da Suleiman Abubakar, kuma a yanzu haka suna samun kulawa a wani asibiti.” Inji shi.

Sai dai duk kokarin da aka yi na jin ta bakin rundunar Yansandan jahar Kaduna game da lamarin ya ci tura, sakamakon kakaakinta, ASP Jalige bai bada wani jawabi game da harin ba.

A wani labari kuma, gwamnan jahar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa daga cikin mutane 59 dake dauke da cutar Coronavirus a jahar Kaduna, 50 daga cikinsu almajirai ne.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a shafinsa na kafar sadarwar zamani na Twitter, inda yace samun almajirai 50 masu cutar yasa jahar ke da muutane 59 dake da cutar.

A lissafin hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC, jahar Kaduna na da mutane 66 da suka kamu da cutar Coronavirus, daga cikinsu har da gwamnan jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel