Yanzu-yanzu: Ganduje ya sassauta dokar kulle a Kano, ya sanar da ranakun walwala
Gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da sassauta dokar hana fita a jihar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka.
A cewar Ganduje, Mutane za su iya fita suyi walwala a ranakun Litinin da Alhamis daga karfe 10 na safe zuwa karfe 4 na yamma kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.
Gwamnan ya bayyana cewa ba za a bude kasuwanni ba sai dai manyan kanti na sayar da kayayyakin masarufi.

Asali: UGC
DUBA WANNAN: Boko Haram: Shekau ya musanta rade-raden zai mika wuya, ya bada sharuddan sulhu
Ganduje ya kara da cewa Kasuwan Yankaba da na Yan Lamo kawai za a rika budewa a ranakun Litinin da Alhamis daga karfe 10 na safe zuwa karfe 4 na yamma.
Wannan na zuwa ne bayan matasa sun yi zanga zanga a birnin ta Kano inda suka koka kan dokar hana fitar.
Masu zanga zangar sun ce ba adalci bane a hana su fita kuma ba a samar musu da isasun kayan tallafi ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng