Siyasantar da Covid-19: Ganduje ya yi wa shugaban NHIS 'wankin babban bargo'

Siyasantar da Covid-19: Ganduje ya yi wa shugaban NHIS 'wankin babban bargo'

- Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Mohammed Garba ya zargi shugaban NHIS, Farfesa Usman Yusuf da saka siyasa a yakar COVID-19

- Kwamishinan ya zargi farfesan da bata wa Gwamna Ganduje suna tare da kokarin tada zaune-tsaye a maimakon tallafawa wajen yakar cutar

- Farfesan ya yi wallafe-wallafe a kafafen sada zumuntar zamani inda yake zargin Gwamna Ganduje da kawo cutar korona yankin arewa

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Mohammed Garba, ya zargi tsohon shugaban NHIS, Farfesa Usman Yusuf da saka siyasa a yaki da cutar coronavirus.

Shugaban NHIS din ya zargi Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da dasa cutar a fadin jihohin arewa, jaridar The Nation ta wallafa.

Ya zargi farfesan da kokarin bata wa gwamnan suna tare da tada tarzoma a jihar a maimakon bada gudumawa wurin magance matsalar.

Kwamishinan yada labaran, ya ce cutar ta bulla wasu jihohin arewa tun kafin a sameta a jihar Kano.

Ya jaddada cewa ta isa jihar Kaduna da wasu jihohi hudu ko biyar kafin ta yada zango a jihar Kano. Ta yaya Gwamna Ganduje ya kawo cutar arewa?

Siyasantar da Covid-19: Ganduje ya yi wa shugaban NHIS 'wankin babban bargo'

Siyasantar da Covid-19: Ganduje ya yi wa shugaban NHIS 'wankin babban bargo'. Hoto daga Pulse.ng
Source: UGC

KU KARANTA: COVID-19: Sheikh Gumi ya aike wa Buhari muhimmin sako a kan sassauta doka

Kamar yadda yace, "Kamar yadda farfesan ya bayyana cewa asibitin Malam Aminu Kano bashi da kayan aiki, toh sanannen abu ne idan aka ce asibitin gwamnatin tarayya ne ba na jiha ba.

"NCDC ce ta samar da dakin gwajin don haka babu ruwan gwamnatin jihar da shi."

"Idan za mu tuna, lokacin da aka rufe dakin gwajin na sa'o'i 74, gwamnan ne ya fito ya roki gwamnatin tarayya da ta hanzarta kawo dauki don mutanenshi na cikin damuwa.

"A komai idan aka duba, za mu ga cewa farfesan ne ke siyasantar da al'amura don bata sunan gwamnan.

"Ya yi wallafe-wallafe a kafafen sada zumuntar zamani amma mun kyaleshi. Wannan ce amsa ta farko da ya fara samu," kwamishinan yace.

A halin yanzu, jihar Kano ce ta biyu a yawan masu dauke da cutar a duk Najeriya. Ta sha gaban birnin tarayya inda take takewa jihar Legas baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel