An bayyana dalilin korar ma'aikatan kamfanin Atiku

An bayyana dalilin korar ma'aikatan kamfanin Atiku

Kamfanin sadarwa Gotel Communications Limited da ke Yola da ya sallami wasu maaikatansa masu yawa a ranar Maiakata ta Duniya wato 1 ga watan Mayu ya bayyana dalilin aikata hakan.

Kamfanin da ke da gidan talabijin da rediyo mallakar tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya ce ya sallami wasu ma'aikatan sa ne saboda wasu sauye sauye da aka fara tun shekarar da ta gabata.

Kamfanin ta mika wa maaikatan ta akall 46 takardar sallama a ranar Jumaa kasancewar ta ranar Ma'aikata ta Duniya.

Kamfanin Atiku ta bayyana dalilin korar ma'aikatan ta 46
Kamfanin Atiku ta bayyana dalilin korar ma'aikatan ta 46. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Boko Haram: Shekau ya musanta rade-raden zai mika wuya, ya bada sharuddan sulhu

Wasu daga cikin ma'aikatan da aka sallama sun ba ce kimanin mutane fiye da hamsin aka kora yayin da wasu suka ce 56 da yi niyyar kora amma daga baya aka rage ya zama 46.

Sanarwar ta aka fitar na bayyana dalilin korar ma'aikatan bai fadi ainihin adadin wadanda aka sallama ba.

Sanarwar mai dauke da sa hannun babban manajan kamfanin, Mohammed El-Yakub ta ce babu hannun Atiku Abubakar cikin sallamar ma'aikatan a ranar Juma'a.

Sanarwar ta ce, "Sallamar wasu ma'aikatan Gotel Communications Limited, da ke karkashin Priam Group sauye sauye ne da aka fara a kamfanin."

Mai kamfanin na Priam ya sanar da wasu matsaloli da kasuwancinsa ke fuskanta hakan yasa aka fara sauye sauye tare da yin maja da wasu kamfanonin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel